Trump ya yi wa jakadan Amurka a Nijeriya da wasu ƙasashe 29 kiranye

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta sauke Jakadan ƙasar a Nijeriya, wato Richard Mills, tare da wasu jakadun ƙasashe guda 29 a duniya, a wani ɓangare na sabon tsarin sake fasalin ofisoshin jakadancin ƙasar.

Blueprint ta ruwaito cewa, ƙasashe 13 na Nahiyar Afirka na daga cikin waɗanda hukuncin ya shafa yayin da Amurka da ɗauki ɗamarar sauya tsarin difulomasiyyarta a ƙasashen waje.

Wannan mataki na cikin shirin Shugaba Trump na tabbatar da manufarsa ta bai wa Amurka fifiko a harkokin difulomasiyya da ƙasashen waje.

Bisa bayanan jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje, waɗanda suka nemi a boye sunayensu, an tabbatar da cewa yawancin waɗannan jakadu an naɗa su ne a lokacin gwamnatin Biden, kuma wa’adinsu zai ƙare a watan Janairu.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan jakadun da aka cire sun fito daga ƙasashen Afirka ciki har da Nijeriya, Burundi, Kamaru, Côte d’Ivoire, Senegal, da Uganda, Ruwanda, Somaliya sai kuma wasu daga Turai, Asiya-Pacific, Gabas ta Tsakiya, Kudancin Asiya, da yankin Yammacin Duniya.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ya bayyana sauye-sauyen a matsayin al’ada a kowace gwamnati, yana mai cewa jakadu wakilan shugaban ƙasa ne, kuma yana da hurumin tabbatar da cewa waɗanda ke wakiltar Amurka a ƙasashen waje suna aiwatar da ajandar gwamnatinsa.

By Babaji