Gwamnan Kano ya ƙaddamar da jami’an tsaro masu sa idanu a yankuna

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta yaye matasa 2000 da suka samu horo a fannin tsaro inda za su yi aiki ƙarƙashin wata hukuma mai sa idanu kan lamuran tsaro a yankunansu.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci bikin rantsar da matasan 2000 da suka kammala samun horo bayan watanni, a bikin da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a jihar Kano, bikin da ya samu halattar dubban al’umma.

A yayin bikin da ya samu halartar gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa da wakilan gwamnonin Kaduna da Zamfara da Sokoto da sauransu an nunar da muhimmancin haɗa kai tsakanin jihohin da ke yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya da a cewar Radda gwamnan na Katsina ya zama wajibi su haɗa kansu don yaƙar wannan bala’i na matsalar tsaro.

“Ba wani ne zai zo daga Enugu ko Fatakwal yace zai gyara mana wannan matsala ba mune daga Kano da Katsina da Sokoto”.

A nasa jawabin yayin taron Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya yaba wa Gwamnan Kano kan wannan yunƙurin samar da tsaro tare da ba wa gwamnan tabbacin haɗin kan sauran sarakunan da hakimai.

Ya ƙara da cewa, “Aikin tsaro bana ɓangare ɗaya ba ne kowa na da rawar da zai taka muddin ana so a cimma nasara.”

Gwamnan Kano da ya bayyana wannan hukumar tsaro da za ta sa idanu kan yankuna a matsayin tallafi ga jami’an ɗamara a mataki na ‘yan sanda da soja da bijilanti da Hisbah da sauransu .Yace za su haɗa kai da jihohi maƙota don daƙile wannan matsala da ke neman zamewa jihohin alaƙaƙai.

Yace shugaban Najeriya ya cancanci yabo a ƙoƙarin da yake na goyon bayan jihohi na ganin sun ƙarfafa tsaron da suke da shi wanda a fatansa nan gaba a tallafa wa jihohin ga batun samar da hukumar tsaro ta jiha.

Bikin yaye jami’an dai, gwamnan ya ƙaddamar da Babura 440 da motoci ƙirar Hilux 88 waɗanda jami’an za su yi aiki su da su wajen tallafawa harkokin tsaro a ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

By ukarofi