
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Ungoggo, Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo ya rasu a yammacin yau Laraba.
Sakataren yaɗa labarai na majalisar, Kamaludeen Sani Shawai ne ya tabbatar da labarin ga BlueprintManhaja.
A cewarsa, marigayin ya samu gajeriyar rashin lafiya ne a yau jim kaɗan bayan ya isa harabar majalisar dokoki, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.
Saidai, daga bisani likitoci a asibitin suka tabbatar da rasuwar Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, abin da ya jefa ‘yan majalisa, iyalai da al’ummar Ungoggo cikin alhini da jimami.
Shawai ya ƙara da cewa, za a gudanar da jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 6 na yammacin yau, bisa koyarwar addinin Musulunci.
Rasuwar Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo ta zo a matsayin babban rashi ga majalisar dokokin jihar Kano da ma al’ummar Ungoggo, inda ake bayyana shi a matsayin ɗan majalisa mai jajircewa da kishin jama’arsa.
Awanni kaɗan bayan rasuwar ɗan majalisar na Ungoggo sai kum rahoton rasuwar Ɗan majalisar jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni, wato Sarki Aliyu Daneji.
Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar na birni.
Saidaihar lokacin hada wannan rahoton ba mu sami labarin dalilin rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji ba.
