Yanzu-yanzu: Mutane da dama sun rasu bayan bom ya tarwatse a Masallacin Juma’a na Maiduguri

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun tada bom a wani masallacin Juma’a da ke Gundumar Gamboru a tsakiyar Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:10 na yamma a yau Laraba yayin da jama’a suke tsaka da sallar Magriba.

Duk da cewa ba a samu cikakken bayani ba game al’amarin yayin rubuta wannan rahoto, mazauna yankin sun shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho cewa da dama daga cikin masallatan sun rasu yayin da wasu kuma suka jikkata.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso ya ce bai tabbatar da al’amarin ba, amma zai halarci wajen tare gane wa idonsa.

Wannan al’amari ya jefa tsoro acikin al’umma musamman Kiristoci duba da cewa suna halin gudanar da shirye-shiryen bikin Kirsimeti.

Tuni jami’an tsaro suka bazama a yankin da abin ya faru domin bada kariya ga sake faruwar irin haka a gaba da kuma yin bincike akan al’amarin.

By Babaji