
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta bankaɗo wasu manyan kadarori guda 41 da aka danganta su ga tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) da ɗansa Abdulaziz Malami, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin gagaruman bankaɗa da aka yi wa tsohon babban jami’in gwamnati.
Manhaja ta ruwaito cewa, kadarorin sun haɗa da jami’o’i, otal-otal, makarantu, cibiyoyin kasuwanci, manyan gonaki da kuma filaye, waɗanda an samo su ne a jihohin Kebbi, Kano da kuma Birnin Tarayya Abuja, inda jimillar kuɗaɗensu ta kai Naira biliyan 212.89.
A wasu takardu da jaridar NewsPointNigeria ta samo, an yi nasarar gano haka ne yayin da EFCC take tsaka da gudanar da bincike akan zargin Malami da hannu a badaƙalar wasu maƙudan kuɗaɗe sakamakon bincike da ta yi akan gidajensa na Abuja da Kebbi a ranar 17 ga watan Disamba, 2025.
Takardun EFCCn sun bayyana cewa kadarorin da aka gano a Kebbi kaɗai a jimillance sun kai na biliyan N162.19, yayin da na Kano suka kai biliyan N16.01, sai kuma Naira 34.69bn ga na Abuja.
Kadarorin na Kebbi ana alaƙanta su ne da sunan ‘Rayhaan da Azbir’ waɗanda suka haɗa da na fannoni kamar na ilimi, lafiya, noma makamashi, kafafen watsa labarai da gidaje.
Waɗanda suka fi daraja aciki sune: “Rayhaan University Permanent Site – ₦56 billion
Rayhaan University Temporary Site – ₦37.8 billion
Rayhaan Model Academy – ₦11.2 billion
Rayhaan Primary and Secondary School – ₦8.75 billion
Azbir Hotel – ₦10.33 billion”, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito.
Haka ma a Jihar Kano, inda galibinsu na walwala da muhallin zama ne, waɗanda suka haɗa da:
“Zeennoor Hotel – ₦11.2 billion
Rayhaan Hotel Kano – ₦2.24 billion
Rayhaan Gym Kano – ₦1.23 billion
Luxury residence, Ahmadu Bello Way – ₦982.8 million.”
Na Abuja kuwa, sune manyan gidaje da otal-otal da kuma rukunin gidaje a manyan unguwanni masu alfarma. Ga su kamar haka: “Meethaq Hotel, Maitama – ₦12.95 billion, Meethaq Hotel, Jabi – ₦8.4 billion, Harmonia Hotels, Area 11, Garki – ₦7 billion, Duplex, Maitama – ₦5.95 billion, 42 housing units, Efab Estate – ₦385 million.”
Kawo yanzu dai Malami ko wakilansa ba su ce koma akan bankaɗar ba a lokacin hada wannan rahoto yayin ita ma EFCC ba ta shigar da ƙara a hukumance ba a game da al’amarin. Saidai, tana cigaba da gudanar da bincike domin ɗaukar mataki na gaba a kai.
