Gasar Tsangayar Gusau ce lamba ta ɗaya a duk gasannin marubutan Hausa – Muntasir Shehu

Spread the love


Gasar Tsangayar Gusau ba kamar Hikayata ba ce – Aisha Adam Hussaini

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gasar rubutun ƙagaggun labarai ta Tsangayar Gusau wanda aka fi sani da Gasar Gusau Institute, ta samo asali ne shekaru takwas da suka gabata, ƙarƙashin kulawar Cibiyar Nazari da Bincike ta Gusau Institute da ke Kaduna.

Tsohon Ministan Tsaron Nijeriya Janar Aliyu Mohammed Gusau shi ne ya ƙirkiro da wannan gasa kuma yake ɗaukar nauyin ta, domin ƙarfafa gwiwar marubuta adabin Hausa. Da kuma samar da litattafan Hausa masu ɗauke da ingantattun labarai da aka tantance su, saboda ajiyewa a ɗakin karatu da bincike na Cibiyar Aliyu Mohammed Gusau dake Kaduna, saboda masu zuwa nazari da karatu a ɓangaren adabi da harshen Hausa.

Tun da aka fara wannan gasa a shekarar a shekarar 2018, kowacce shekara Cibiyar na bai wa marubutan Hausa, ba tare da ƙayyade shekaru ko ware wani jinsi ba, damar bayyana basirar su da gogewarsu a fagen ƙirƙirar labari, da isar da saƙonni masu muhimmanci, don gyara kayanka, ga al’ummar Hausawa da masu nazarin harshen Hausa.

A wannan shekara ta 2025 kamar sauran shekarun baya, an samu marubuta masu himma da suka shigar da labaransu cikin wannan gasa ta Tsangayar Gusau, har guda ɗari da sittin da biyar. Sai dai kamar yadda yake bisa tsarin gasar, a matakin farko ana shigar da tsakure ne daga labarin da marubuci ke son ya gabatar, domin zama somin taɓi, yadda zai ja hankalin alƙalai har su bashi damar gabatar da cikakken labarin a matsayin littafi guda, cikin wasu ƙayyadaddun kalmomi, inda ake ware labarai guda goma sha biyar da suka fi ɗaukar hankali. Daga bisani kuma sai a kai ga matakin tantance littattafan da suka fi ma’ana da inganci, ta fuskar zubin labari, kiyaye ƙa’idojin rubutu, da yadda marubucin ya yi amfani da basira wajen warware saƙonnin da yake son isarwa ga mai karatu. Wannan shi ne yake kai wa matakin ƙarshe, inda ake ware gwarazan labarai guda uku da aka tantance, kuma aka yarda da cancantar su.

Aisha Adam Hussaini, wacce aka fi sani da Ameera, daga Jihar Kano, ita ce ta zo a matsayi ta farko da labarinta mai suna ‘Tuwon Makauniya’, inda ta samu kyautar Naira dubu 250. Yayin da Muntasir Shehu, marubucin littafin ‘Haihuwar Guzuma’, ɗan Jihar Kano ya samu zama gwarzo na biyu da labarinsa mai suna, ‘Cinikin Rai’, tare da samun kyautar kuɗi Naira dubu 150. Gwarzuwa ta uku ita ce Hafsat Ibrahim Khalil marubuciyar littafin ‘Makauniyar Soyayya’, daga Jihar Kaduna, wacce labarinta na ‘Amosanin Jini’ ya zama na uku, kuma ta samu kyautar Naira dubu ɗari.

Littafin ‘Tuwon Makauniya’, yana ƙunshe ne da labarin wata jajirtacciyar uwa, wacce ta tsinci kanta da jarabtar hallitar gemu a fuskarta. Sai ya zama mutanen karkarar da take rayuwa da su sun kafa mata ƙahon zuƙa, haɗe da jifanta ta kalmar maita, musamman ga duk wani bala’i da zai faru sai su dangatata da shi, cikin wannan yanayin. Sai Allah Ya ƙaddari ta haifi yaro mai ɗauke da wata larura saboda rashin yin awon ciki. Daga ƙarshe suka danganta jaririn da cewar ɗan ruwa ne, har suka yi yunƙurin jefa shi a kogi. Hakan ya sa ta ƙeƙasa ƙasa ta ɗauke ɗanta ta bar garin da shi. Labarin yana ƙunshe da darussan hannunka mai sanda; da wayar da kan al’umma ta fannoni da dama da suka shafi muhimmancin haihuwar ‘ya’ya mata, illar aikatau, illar camfi da ƙyamar mai wata lalura, da sauransu.

Labarin da ya zo na biyu kuwa, shi ne ‘Cinikin Rai’, labari ne da ya ƙunshi yadda sauyin rayuwa daga rufin asiri zuwa ƙunci da tsanani ya sanya wani mutum zaɓar sayar da wani sashe na jikinsa wanda kuma hakan ya zamo silar sheƙawarsa barzahu, dalilin mutuwar tashi kuma ta zama silar bankaɗowar asirin wasu mutane masu aikin safarar sassan jikin mutane zuwa wata ƙasar Turai.

‘Amosanin Jini’, shi ne sunan labarin da ya samu zama na uku, wanda Hafsat Ibrahim Khalil ta rubuta. Yana ɗauke ne da labarin wata likita da ta tsinci kanta cikin wani ruɗani, bayan bayyanar cutar sikila a jikin ‘yarta alhalin ita AA ce mijinta kuma AS. Lamarin ya ƙara ta’azzara ne biyo bayan gwajin DNA da ya tabbatar ‘yar ba jininta ba ce amma jinin mijinta ce. Wannan dalilin ne ya ankarar da ita hanyar da ta bi wajen ɗaukar cikin. Daga ƙarshe, duk da ƙalubale tare da tsananin ciwo yarinyar ta zama abar kwatance a duniya.

Dukkan waɗannan marubuta dai sun bayyana matuƙar farincikinsu da muhimmiyar nasarar da suka samu, wacce suka kwatanta da muhimmiyar dama, da sai mai rabo ke samu. Duk kuwa da kasancewar dukkansu ba sabbin shiga ba ne a harkar rubutu, kuma sun sha samun nasara a gasanni daban-daban. Kamar ita garzuwar wannan shekara ta farko, Aisha Adam Hussaini, wacce ta ma taɓa zama Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa a shekarar 2023.

A cewar Aisha Ameera, “A gaskiya gasar Gusau ta sha banbam da ragowar gasanni har Hikayata, duba da adadin yawan kalmomin zuwa tsarin gasar. Domin a yanayin tsarin gasar Gusau duk labarin da za a shiga da shi, kowanne irin jigo aka ɗauka yana buƙatar ka tsaurara bincike, ta yadda za a faɗaku kuma a ilimantu.”

Shi kuwa gwarzo na biyu, kuma harwayau gwarzo na biyu a Gasar Bashir Othman Tofa ta Kano Book Club a wannan shekara, Muntasir Shehu wanda ya fito daga ƙungiyar Kainuwa Writers Association, cewa yake yi, “Haƙiƙa farin cikin da na ji a lokacin ba zai misaltu ba, ranar nan ta shiga cikin ranaku masu matuƙar muhimmanci da ɗimbin tarihi a cikin rayuwata. Na ji farin ciki sosai, don zan iya cewa Gasar Gusau ita ce gasar da babu kamar ta. Zan iya saka ta a matsayin lamba ta ɗaya a dukkan gasannin rubutun Hausa da ake sanyawa a wannan ƙasa, domin kuwa ita gasa ce wadda bayan tsanani rabo ma to, dole sai da ƙwarewa sannan mutum zai iya kai wa gaci, domin gasa ce wadda wani ba zai rubutuwa wani ba.”

A cewar, Hafsat wacce ta fito daga Karamci Writers Association, “Zan so a ce masu shirya wannan gasa za su ɓullo da wani tsari da za a riƙa horar da waɗanda suka tsallake matakin farko don koyar da dabarun rubutu da ƙirƙira. Hakan zai ƙara wa marubuta masu sha’awar shiga wannan gasa ƙarfin gwiwa da ingancin ayyukan da za a gabatar.”

Ra’ayinta ya zo daidai da na abokin karawarta Muntasir, wanda ya ce, “Zan so a ce sun ƙirƙiri wani tsari na bai wa gwarazan gasar horo na musamman a kan dabarun inganta rubutu duk shekara, bayan kammala gasar, domin ƙara ƙarfin gwiwa ga gwarazan da ma masu son shiga gasar.”

Gwarazan sun bai wa sauran marubuta da har yanzu ba su kai ga samun nasara ba shawarar da su cigaba da gwada sa’ar su, kuma su ƙara da addu’a, domin nasara daga Allah take. A cewar Hafsat, “Sirrin nasara shi ne zaɓen jigo mai ma’ana tare da yin sahihin bincike a kansa, sannan a jingina komai da addu’a.’ Ita kuwa Ameera cewa take yi, “Shawarar da zan bai wa marubutan da ke burin shiga gasar Gusau ita ce, su nemi jigo mai kyau da zai wayar da kan al’umma. Su kuma tsaurara bincike a kansa, su tsara zubi da tsarin labarin. Bayan sun kammala su bayar a duba musu, domin hango kuskuren da su ba su gano ba. Sai kuma addu’a, ita ce uwa-uba, su dage da addu’a idan da rabo za a dace.”

A ta bakin Muntasir, “Shawarata ba za ta wuce in ce a ƙara jajircewa ba, rabo yana tafe muddin aka jajirce, kafin in kai ga yin nasara a wannan shekara sai da na shiga gasar sau biyar sannan Allah ya ba ni ikon hayewa. Don haka kar a sare, nasara tana tafe. Sirrin gasar nan bai wuce jajircewa da dagewa da addu’a ba, sai kuma ƙoƙarin yin ingantaccen rubutu da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗawa gasar.’

Yanzu dai babban burin Muntasir a nan gaba shi ne, a samar da gasar Hikayata ta maza to, wacce a nan ne zai ƙara zagewa ya nuna basirar sa. Ita kuwa Ameera burinta shi ne, ta yi nasara a Gasar ɗangiwa. A wajen Hafsat kuwa, abin da take buri a matsayinta na marubuciya, shi ne duk gasar da ta shiga a ce ita ce ta yi nasara!

By ukarofi