Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An kuma umarci makarantun da aka buɗe da su nemi sahalewar NBTE cikin watanni uku na sabuwar Shekara.
Haka kuma gwamnatin jihar ta rufe makarantu 17 tare da wasu biyu da aka gano suna karantawa ba tare da ƙa’ida ba.
Mai ba gwamna shawara kan makarantun lafiya Hon. Umar Mammada ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai kan matakin da gwamnati ta ɗauka domin kawo gyara a ɓangaren lafiya.
Ya ce gwamnati ta kuma bada umarnin kada kowane asibiti da ke mallakin jihar ya amshi ɗalibai dan koyar dasu, har sai sun samu amincewa daga Gwamnati.
Ya ƙara da cewa, dukkanin matakan da gwamnati ta ɗauka, tayi su ne domin kawo gyara a ɓangaren lafiya na jihar Katsina baki ɗaya.
Daga cikin makarantun da aka buɗe akwai Alliance College of Public and Environmental Health, Shema, inda aka bata damar ta karantar da kwasa-kwasan Bio-medical and Pharmacy Technician.
Sai GIAL College of Health Science an bata damar karantar da kwasa-kwasan CHEW, Pharmacy Technician, Medical Laboratory da Environmental and Health Information Management.
Akwai kuma Cognate Community College of Health and Technology inda aka bata damar ta karantar da kwas ɗin CHEW kaɗai.
Hakanan akwai, KEBRAM College of Health Sciences and Technology Katsina, inda aka bata damar karantar da kwas guda, kwas ɗin CHEW.
Sai Barda College of Health Sciences Katsina, itama gwamnati ta ba ta damar karantar da kwasa-kwasan CHEW da J-CHEW kaɗai.
Hakanan, mai ba gwamna shawarar ya bayyana cewa dukkanin waɗannan makarantun guda biyar da aka buɗe da wasu guda tara da aka buɗe tun a farko da su yi gaggawar nemo sahalewar NBTE-Accreditation kafin nan da watanni uku na farkon sabuwar Shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa, a lokacin kwamitin da gwamna ya naɗa ya ke bincike ya kuma gano wasu makarantu guda biyu da suke buɗewa ba tare da ƙa’ida ba, inda aka kulle su nan take, da suka haɗa da Sabo Musa College of Computer and First aid Management.
