Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi wasu kalamai a kwanan bayan nan, inda ya buƙaci ’yan jam’iyyar NNPP su yi mubaya’a ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, ya jawo kace-nace da musayar yawu kan dambarwar masarautar Kano.
A ranar 23 ga Mayu, 2024, gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya tuɓe Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bayan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta soke dokar masarautar ta shekarar 2019, wacce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya kafa.
Majalisar ta dawo da Sarki Sanusi kan karagarsa. Sai dai Aminu Bayero ya ƙalubalanci gwamnatin a kotu da ci gaba da zaman fada a gidan sarki na Nasarawa da ke cikin birnin Kano.
A yayin da yake magana a ranar Talata a wurin bikin ƙaddamar da dakarun tsaron na jihar Kano da aka kira da “Neighbourhood Watch Corps (NWC)”, Kwankwaso ya buƙaci ’yan Kwankwasiyya su miƙe tsaye su yaƙi abin da ya kira da ƙarfafa-ƙarfafar Gwamnatin Tarayya ta ƙaƙaba Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano.
“Sarki ɗaya ne da mu a Kano, kuma Ina son ku shaida shine Sanusi Lamiɗo Sanusi,” Kwankwaso ya faɗa a filin wasa na Sani Abacha.
Lamarin siyasa a Kano ya ɗau zafi tun da fari tun bayan toshe dukkan hanyoyin da za su kai mutum zuwa gidan gwamnati.
A wurin taron, wanda shi ma Sarki Muhammadu Sunusi II ya halarta, Kwankwaso ya buƙaci kwanishinan ’yan sandan Kano da ya gaggauta janye ’yan sandan da suke gadin Sarki Aminu Ado, yana mai cewa, zamansu a wurin yana tayar da hankalin al’umma. Sannan ya bayyana ci gaba da zaman sarkin a matsayin ƙalubale ga masarautar Kano.
A cikin wani martani da ya yi, Aminu ɗan’agundi, wani basarake a Kano, ya yi Alla-wadai da kalaman Kwankwaso da kalamai na tunzuri da kin biyayya ga umarnin kotu.
A yayin da yake magana da gidan rediyon Lumana, ɗan’agundi, wanda ya shigar da ƙara tun da fari yana ƙalubalantar soke dokar masarauta da Gwamna Abba ya yi, ya jaddada cewa Aminu Ado bai saɓa kowacce iriyar doka ba na zama a wannan gidan sarautar ba, yana mai cewa gwamnatin Kano ta ƙi ba shi damar kare kansa.
“Muna ƙalubalantar matakin gwamnatin Kano a kotu. Kotu ta riga ta yi hukuncin cewa cire sarkin ya saɓa wa doka tare da jaddada cewa ya ciga ba da zamansa a matsayin sarki,” ya bayyana.
Ya kuma ce, ko da ba ‘yan sanda, muna da ikon gayyato dubin nan matasa da za su bai wa fadar tsaro. Idan da sarautar ana kaɗe ƙuri’a, to, da lallai za mu ka da Kwankwaso da mutanensa.”
Ya kuma yi kira ga magoya baya da zu cigaba da nuna ƙarfin guiwarsu kan cewa nan ba da daɗewa ba, sarki Aminu Ado zai dawo kan kujerarsa.
Wannan rikici dai ya samo asali ne tsakanin jagoran Kwankwasiyya Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Tun da farko, a shekarar 2014, Kwankwaso ya naɗa sarkin Sanusi a matsayin gwamnan Kano a shekarar 2020, sai dai Ganduje ya sauke shi yana buga hujja da rashin biyayya inda ya tsaga masarautar Kano gida biyar domin raunata ƙarfin ikon sarkin inda ya naɗa Aminu Ado a matsayin sarki.
A shekarar 2024, yaron Kwankwaso a siyasa, Yusuf, ya soke matakin Ganduje, kuma ya ce, an ɗauki matakin ne domin “dawo da martabar” tsohuwar masarautar da cika alƙawarin yaƙin neman zaɓe da ya yi wa al’umma.
Gwamna Yusuf ya yi amfani da dokar da majalisar dokokin Kano suka yi wajen dawo da sarki Sunusi II.
Sarkin da aka dauke dai ya dogara ne da hukuncin babbar kotun tarayya wacce ta ce tsarin da aka bi wajen sauke sarkin ya saɓa wa ‘yancinsa.
Kalaman Kwankwaso dai sun ƙara fito da takun tsaka da ke tsakanin gwamnatin Kano ta jam’iyyar NNPP da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jam’iyar APC.
A yanzu dai wannan magana na gaban kotun ƙoli wacce za ta yanke hukunci na ƙarshe kan dambarwar.
