Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani mai fafutukar kare haƙƙin jama’a kuma mai neman takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a jihar Yobe, Barr. Kashim Musa Tumsah(KMT) ya bayar da gudummawar abinci iri-iri ga reshen mata na ƙungiyar kiristocin Najeriya CAN a Yobe domin su gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekarar cikin sauƙi.
A cewar mai magana da yawun sa, Abubakar Ahmed a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau, ya ce wannan tallafin wani ɓangare ne na gudummawar da ya bayar domin murnar bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Abubuwan da ya bayar sun haɗa da buhunan shinkafa sama da ɗari, kwalaye na taliya da sauran kayan abinci.
A cewar sanarwar, tuni an miƙa wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin ta hannun wakilan KMT a Damaturu, babban birnin jihar.
Tumsah, babban mai fafutukar ci gaba a jihar, ya bukaci Kiristoci da su cigaba da bin hanyoyin ‘yan uwantaka wajen rayuwa cikin lumana da kowa a jihar.
Ya tabbatar da cewa idan ya zama gwamnan jihar a shekarar 2027, za a gabatar da ƙarin kayan tallafi don amfanin jama’a da gamsuwarsu.
Da take karɓar kayan, shugabar ƙungiyar kuma mai kula da harkokin ƙungiyar Haske Forum CAN, Mrs Sarah Marcus ta yaba masa da wannan taimako.
Ta tabbatar da cewa dukkan membobin da suka fito daga yankunan sanata uku na jihar za su amfana da tallafin bisa tsari da adalci.
