Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya amince da rabon kuɗaɗe sama da Naira Miliyan 500 ga al’umma daban-daban na ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin Jihar Katsina.
Mai ba gwamnan shawara kan harkokin jam’iyyu, Hon. Shafi’u Audu Duwan ne ya jagoranci ƙaddamar da wannan shiri na rabon tallafin ga al’ummar ƙananan hukumomin jihar baki ɗaya.
An ƙaddamar da shirin ne a ƙarƙashin ofishin mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa,Rt Hon. Ya’u Umar Gwajo- Gwajo a matakin ƙananan hukumomi.
Yawancin mutanen da suka amfana da tallafin shugabannin jam’iyar APC a mataki da ban da ban.
Sun haɗa da shugabanni na matakin jiha da na ƙananan hukumomi.
Sai shugabanni na kananan hukumomi da na gundumomi da sauran su.
Jagoran rabon tallafin kuma mai ba gwamna shawara kan jam’iyu Hon Shafi’u Audu Duwan ya shaidawa manema labarai cewa babu shakka wannan karamci na malam Dikko Raɗɗa zai taimaka wa shugabannin jam’iyar wajen ƙara tallatar da jam’iyar ga al’ummar jihar.
Duwan yayi kira ga ya’yan jam’iyar da su cigaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya musamman ganin lokacin zaɓe na ƙaratowa.
