Bichi: Sarkin Kano ya nemi sabon Dagacin Hagawa ya kiyaye adalci

Spread the love

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II ya ja hankalin Sabon Dagacin garin Hagawa, Malam Mansur Abdur-Rahman na Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, akan ya zamo mai adalci da riƙon amana a wajen jagorantar al’ummarsa.

Sarkin ya bayyana haka ne a anar Talata jim-kaɗan bayan da aka nada sabon dagacin a Fadar sarkin.

Mai Maraba Sanusi na II ya gargaɗe shi game da haɗa kai da azzaluman mutane masu cutar da al’uma ta kowace siga.

Ya tabbatar masa da cewa wannan nauyi ne da Allah (SWT) ya dora masa. Ya kuma shawarce shi da bude zauren shawara da zai kyautata rayuwar al’uma yadda yakamata.

A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, ta ce tun da fari sabon dagacin ya tsallake dukkan sharuda na tantance shi ne sakamakon nagarta ta kyawun dabi’unsa tare da ilimin addini da boko da yake da su.

Kazalika mutane ashirin 20 suka ba da shawarar cancantarsa da suka hada da; Limamin Hagawa cikin gari, Malam Yakubu Usman sai Mai Unguwar cikin gari, Malam Lawal Usaini da Sarkin Fulani, Alhaji Magaji Umar da sauransu.

“Jama’a kun ji abin da Hakimi ya rubuto, haka ne in ji Sarki?” Fadar mai martaba Sarkin Kano.
“I, wannan haka yake!” Al’umar yankin Hagawa dake Bichi.

“Wadanda aka ambaci sunansu da aka yi shawara da su, haka ne in ji Sarki?” Fadar mai martaba Sarkin Kano.
“Haka yake ranka ya dade!” Al’umar yankin Hagawa dake Bichi.

Malam Miko AbdulHamid da ya yi magana a madadin jama’ar yankin Hagawa, sun yaba tare da gode wa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II da kuma Hakimin Bichi Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi sakamakon tabbatar da wannan nadi bisa adalci da cancanta.

“Mai martaba ya tabbatar da cewar kanmu a hade yake, haka ‘ya’yan masarauta su ma kansu a hade yake, saboda haka muna masa godiya Allah ya kara masa lafiya, Allah ya taimaki Sarki. Muna godiya kuma ga dukkan al’uma da suka rako mu. Allah ya saka da alheri!” In ji shi.

Sabon Dagacin, ya yi alkawarin aiki tukuru da zai inganta al’amuran yankinsa ta hanyar biyayya ga kyawawan shawarwarin da ya rabauta da su a fadar mai martaba Sarkin Kano.

“Na dauki alkawari in sha Allahu zan yi dukkanin wani aiki wanda zai zamanto cigaba ne ga al’umata, musamman saboda na san Annabi (SAW) ya ce. ‘Shi shugaba shi ne mai hidima ga al’umarsa.’ Saboda haka zan yi iya yina wajen ganin na yi wa al’umata hidima in sha Allahu. Kawai abin da nake fata da su; hadin-kai da zaman lafiya da goyan baya da kuma shawarwari a dukkanin sadda suka ga na kauce, domin Annabi (SAW) da kansa yana neman shawarar sahabbansa ballantana kuma ni, don haka ina so duk wanda ya ga wani abu ya ba ni shawara”, inji shi.

By Babaji