Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Girma Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Hadiza Bala Usman, wato mai ba sa shawara na musamman akan tsare-tsaren harkokin gwamnati kuma Shugabar Cibiyar Isar da Sakamakon Tsare-tsare (CRDCU) bisa gagarumar gudumawarta ga hidimar ƙasa yayin da take cika shekaru 50 a duniya.
A wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Hadiza a matsayin “jajirtacciyar mai kishin ƙasa” wadda aikinta na kusan shekaru 30 a gwamnati ya zama abin misali ga al’umma sakamakon sadaukarwa da himmarta ga ci-gaban ƙasa.
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa ƙoƙarinta na aiki a Hukumar kula da kadarorin gwamnati inda ta nuna hangen nesa da fahimta na daidai ga muhimman gyare-gyaren tsarin ci-gaban harkar tattali.
Haka kuma ya yaba wa gudumawarta na Hukumar Kula da kadarorin birnin tarayya, yana mai bayyana hakan a matsayin babban mataki ga zangon aikinta inda ta nuna ƙwarewa wajen kiyaye gaskiya da adalci ga harkokin al’umma.
Kazalika, Tinubu ya yabi hidimarta a harkar siyasa musamman cikin jam’iyyar APC wajen shirye-shirye da harkokin ci-gaba, lamarin da ya taimaka wajen inganta lamuranta na cikin gida da ƙarfafa darajojin dimukraɗiyya.
A ƙarshe, ya kammala da yi mata fatan cigaba da samu ƙwarin gwiwa, hikima, lafiya da ikon tafiyar da al’amuran ayyukanta, waɗanda abin kwaikwayo ne ga mata, matasa da kuma jagororin ƙasa.
