Tashin farashin kuɗin jirgin sama a Disamba bai da alaƙa da haraji – NCAA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) ta musanta iƙirarin cewa harajin gwamnati ne ya haddasa tashin farashin tikitin jiragen sama na cikin gida da aka samu a watan Disamba.

Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin masu amfani na hukumar, Michael Achimugu ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ a ranar Lahadi.

A cewarsa, ƙaruwar farashin ta samo asali ne daga yanayin kasuwa, inda yawan buƙatar tafiya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke haifar da tashin farashi.

Ya ce wannan lamari abu ne da ke faruwa a kowace shekara, kuma ba jiragen sama kaɗai ba ne ke fuskantar irin wannan hauhawar farashi a lokacin bukukuwan ƙarshen shekarar.

Achimugu ya ƙara da cewa ana sa ran farashin zai fara raguwa a watan Janairu, musamman bayan mako na biyu, yayin da buƙatar tafiya ke raguwa.

“Yanayin kasuwa ne kawai. ‘Yan Nijeriya  ne ke yi wa junansu. Ba laifin gwamnati ba ne. Farashin jiragen sama a Disamba ba shi da alaƙa da haraji ko kaɗan. Haraji ba su ƙaru a Disamba ba, kuma da alama farashin zai ragu bayan mako na biyu na Janairu,” inji shi.

By ukarofi