LNT hanya ce ta fasaha da matasa ke samun aikin yi mai armashi — Ambasada Jidda Washa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Jakadiyar fasahar sadarwa ta LNT (Leave No Trace) a Jihar Kano, Ambasada Hauwau Adam Suleiman, wadda aka fi sani da Ambasada Jidda Washa, ta bayyana cewa fasahar LNT wata hanya ce ta zamani da ke bai wa matasa damar samun aikin yi mai armashi da bunƙasa tattalin arziƙinsu.

Ta bayyana hakan ne yayin taron horas da matasa daga jihohin Kano, Katsina da sauran jihohi, wanda aka gudanar a Gidan Tunawa da Malam Aminu Kano, Mumbayya, da ke unguwar Gwammaja a Kano.

Ambasada Jidda Washa ta ce a halin yanzu, fiye da matasa 30 suna aiki ƙarƙashinta ta hanyar fasahar LNT, inda suke samun kuɗaɗe masu kyau cikin ɗan gajeren lokaci. Ta ce sabon tsarin da suka bullo da shi ya sa ake kammala ayyuka cikin sauri fiye da da.

Ta jaddada buƙatar matasa su jajirce wajen koyon fasahohin zamani, tare da bin ƙa’idojin ƙasa, domin cin gajiyar damar aikin yi da tattalin arziƙi da fasahar zamani ke samarwa.

A nasa jawabin, Ambasada Abdulhakim Yusuf daga Jihar Katsina ya ce fiye da matasa 100 ne suka halarci taron, inda aka horar da su dabarun sabunta amfani da fasahar LNT, wadda yanzu ke ba da damar aiwatar da manyan ayyuka cikin saƙonni kaɗan.

By ukarofi