Gwamnonin Arewa sun yi tir da harin kasuwar Neja, sun jajenta hatsarin kwale-kwalen Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF) ta yi alla-wadai da mummunan harin ‘yan ta’adda a Kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Borgun Jihar Neja, tana mai bayyana hakan a matsayin “rashin tausayi akan ‘yan ƙasa da ba su da laifi da kuma babbar barazana ga zaman lafiya da zamantakewar al’umma”.

Rahotanni sun bayyana cewa, aƙalla sama da ƙananan ‘yan kasuwa 30 da suka haɗa da mata da maza ne aka yi wa kisan gilla, yayin da aka yi awon-gaba da wasu da dama tare da ƙone kasuwar da sace kayan abinci daga ‘yan ta’addar.

A wata takarda da NSGF ta fitar ta hannun Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya a madadin takwarorinsa, ƙungiyar ta bayyana kaɗuwarta game da al’amarin, inda ta ce hakan babban iftila’i ne ga iyalansu, harkokin kasuwancinsu da kuma barazana ga yankunan da ke zaman lafiya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa ire-iren munanan ayyukan na rashin hankali da ke harin ƙananan ‘yan kasuwa mata da maza da jama’ar gari da ke gudanar da halattatun ayyukansu, lahani ne da ke zama barazana ga haɗin kai da harkokin tattali.

Ya kuma yi tir da maharan da dukkan masu hannu aciki, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar farauto tare da kamo dukkan waɗanda aka samu da laifi acikin ɗanyen aikin domin su fuskanci hukuncin doka.

Haka kuma, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalai, gwamnatin jihar da kuma yankunan da iftila’in ya afka wa tare da fatan samun rahamar Ubangiji ga waɗanda suka rasu, da kuma fatan ceto waɗanda ke hannun ‘yan ta’addar cikin aminci.

Kamar haka ne a wani ɓangaren, NSGF ta yi jimamin hatsarin kwale-kwalen Jihar Yobe wanda ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 25 yayin da ake cigaba neman wasu 14 da ba a gani ba.

Al’amarin ya faru ne a wani kogin Yobe da ke Ƙaramar Hukumar Nguru a lokacin da mutanen suke dawowa daga harkokin kasuwancinsu.

A madadin takwarorin nasa, Inuwa Yahaya ya jajenta wa iyalai da makusantan waɗanda al’amarin ya rutsa da su, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da ke tunatar da buƙatar fifita tsaron lafiyar al’umma yayin kowane irin sufuri.

A ƙarshe, ƙungiyar ta kirayi al’ummar Nijeriya da su cigaba da zama a dunƙule wajen taimakekeniya a tsakaninsu musamman a lokutan jimami, yana mai jaddada ƙoƙarinsu na aiki da hukumomi masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

By ukarofi