Kotu ta soke rushe jagororin NNPP a Kano, ta jaddada halascin ‘yan ɓangaren Gwamna Abba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotu a Kano ta soke hukuncin rushe majalisun zartarwar NNPP a matakin jiha, ƙananan hukumomi da gundumomi daga ɓangaren kwamitin ayyukan na ƙasa (NWC) na jam’iyyar.

A wani hukunci da Mai Shari’a Nasiru Saminu ya yi a ranar Talata, kotun ta kuma haramta wa kwamitin ɗaukar wani mataki akan tsarin shugabancin jam’iyyar a Kano har sai an gudanar da shari’ar ƙarar da aka shigar akan al’amarin.

Wani mai suna Abdullahi Zubairu Imam da wasu mutane biyar ne suka shigar da ƙarar a madadin kwamitin zartarwar NNPP na ƙananan hukumomi 44 na jihar akan NNPP na ƙalubalantar hukuncin sokewar.

Alƙalin ya umarci dukkan ɓangarorin da su kiyaye sharuɗɗan da kotu ta gindaya a ranar 30 ga watan Disamba, 2025 gabanin umarnin rushewar da NWC na jam’iyyar ya yi.

A kwanakin baya ne NWC na NNPP ya ayyana rushe majalisar zartarwar jam’iyyar a kowane mataki na jihar Kano bayan dakatar da Hon. Hashim Dungurawa a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar. An kuma maye gurbinsa da Abdullahi Abiya.

By Babaji