Gwamnan Zamfara ya zargi Matawalle da amfani da ofishin Ribaɗu wajen garkuwa da jami’in gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta koka game da zargin sace ɗaya daga cikin jami’anta a Abuja, inda ta zargi an yi amfani da jami’an tsaro na tarayya wajen cin mutunci da matsa wa ‘yan ɓangaren adawa a jihar.

Gwamnatin ta yi ikirarin jami’an tsaron birnin Abuja da ke aiki a ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) sun yi garkuwa da Salim Abubakar, wanda mataimakin harkokin gudanarwa ne na ofishin Gwamnan Zamfara,

A wata takarda daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, gwamnatin ta ce al’amarin ya ƙara ƙarfafa damuwa akan yadda ake amfani da hukumomin gwamnatin tarayya wajen takura wa ‘yan ɓangaren adawa.

A cewarta, an ƙaddamar da garkuwar ne ba tare takardar izinin kamu ba daga cibiyar tsaro ta musamman da ke aiki a ofishin NSA.

Gwamnatin Zamfarar ta kuma zargi Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da kitsa awon-gaba da jami’in, lamarin da ta ce shi ya fi tayar da hankali acikin al’amarin.

Haka kuma, ta yi zargin an kai jami’in wani waje da ba a san ina ne ba kana daga bisani aka yi ta sauya masa wurare, wanda ke nuna yunƙurin ɓoye ainihin inda yake da kauce wa adalci.

Akan haka ne ta yi gargaɗin al’amarin matuƙar ba a ɗauki mataki a kai ba ka iya zama barazanar ga ƙwarewa a harkokin tsaron Nijeriya.

By Babaji