Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakarun sojin Nijeriya da ke aiki a karkashin rundunar ‘Operation FANSAN YAMMA OPFY’ sun ceto mutum shida yayin da suke gudanar da ayyukkan su na samar da tsaro a yankin Kajuru zuwa Kujama dake ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Wata majiya mai tushe a rundunar sojin ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN cewa jami’an tsaron sun ceto wadannan mutane bayan rundunar Sub-sector 5 ta sanar da su harin da maharan ke yi a yankin da misalin karfe 9:30 na safe ranar 5 ga Janairu 2026.
Majiyan ya shaida cewa jami’an tsaron sun samu bayanin cewa maharan na kokarin zuwa tsaunikan dake Kasso domin kwaso kayan aikin su da ababen hawansu.
A dalilin haka dakarun suka bisu tsaunikan inda suka yi batakashi da maharan da ƙarfe 10:30 na safe.
“Jami’an tsaron sun yi batakashi da maharan inda da dama daga cikin maharan suka gudu cikin dajin Kasso.
“Jami’an tsaron sun yi kokarin bin maharan domin ganin sun kamo su amma suka kasa domin da dama daga cikin su sun gudu kafin jami’an tsaron su iso inda suke. Sai sai kuma maharan sun gudu sun bar mutum shida da suke tsare a hannun su.
Mutanen da aka ceto sun hada da Maryam Sani mai shekara 40, Saratu Ibrahim ‘yar shekara 20, Abubakar Lawal mai shekara 50, Tukur Sani dan shekara 20, Douglas Tanko dan shekara 18 da Akyala Tanko dan shekara 20 Kuma duk mazauna kauyukan daban daban a jihar Kaduna.
Majiyan ya ce jami’an tsaron sun damka mutanen da suka ceto ga hannun jami’in karamar hukumar Chukun da masarautar Kajuru domin hada su da iyalansu.
