Gombe: Manoma sun koka kan yadda wata dorinar ruwa ke lalata musu amfanin gona

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Wasu manoma da ke garin Hinna a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba a jihar Gombe sun nuna damuwarsu game da wata dorinar ruwa da ke kai wa gonakinsu farmaki da takura wa rayuwarsu.

Zakari Ladan, shi ne shugaban manoma a garin Hinna ya bayyana damuwarsu a yayin hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Litinin.

Ladan ya ce harin da dorinar ruwan take kai musu ya jawo musu asara mai yawa, yana mai cewa suna yawan samun dabbobi suna lalata musu amfanin gona da barazana ga mazauna garin.

Ya ce, yawan dorinar ruwan da ke yankin ya karu zuwa sama da 40 inda suke dirar wa gona wanda hakan ke shafar manoma da masunta.

A cewarsa, daga Satumbar 2025 zuwa yau, dabbobin sun lalata filin noman da ya kai kadada 100 da ake noma hatsi daban-daban da ga ayyaye.

Ladan ya ce, nau’in kayan amfanin gona da suke lalatawa sun haɗa da: shinkafa da kabeji da masara da karas da kuɓewa da kankana da albasa da ganyaye. Sun ce ana ƙiyasin dabbobin sun jawo asarar da ta kai Naira miliyan 180.

“Muna cikin damuwa sosai da irin ɓarnar da dorinar ruwan suke yi mana ta hanyar lalata gonakinmu da cuzguna wa rayuwarmu.”

“A halin yanzu, adadin dabbobin nan sun haura 40. Suna lalata mana shukoki da kashe mutane.”

“Daga watan Satumba zuwa yau, sun kashe mutane 3 a garin nan namu a yayin da wasu uku suka samu raunuka kuma suna kwance a asibiti a Gombe.”

“Idan ka zo garinmu, za ka ga dorinar ruwa na yawo sasakai a gonakinmu. Dorinar ruwa guda ɗaya za ta iya lalata kadada biyu a rana ɗaya.

“Muna nema ɗauki domin tseratar da rayuwarmu saboda irin asarar da muke yi a kullum,” ya bayyana.

Wani manomi, Malam Haruna Hinna, ya ce, sun sun lalata gonar karas ɗinsa da okro domin iya gonar da na ke noman caras an yi asarar da ta kai Naira miliyan N1.7.

Manoma a garin Hinna sun tabbatar da cewa suna yin asara duk da shigar da rahoto ga gwamnatin jihar da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da ma sauran masu ruwa da tsaki.

“Muna neman agaji daga wajen gwamnatin tarayya da ta jiha. Mun gaji da irin halin da muke ciki da ke shafar tattalin arzikinmu.”

Sauran manoman da suka tattauna da NAN sun ba da labarin halin da suke ciki tare da riƙon gwamnati da ta tallafa da kuma ba su kayan aikin gona domin su koma gona.

By ukarofi