Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Kungiyar Tsofaffin ɗaliban Government Technical College (G.T.C) Ungoggo ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ware ɗaruruwan miliyoyin naira domin sabunta makarantar. Wannan yabo ya fito ne a yayin taron ƙungiyar na ƙasa da aka gudanar a harabar makarantar a makon da ya gabata, inda mambobin ƙungiyar UNTOBA suka bayyana matakin a matsayin hujja ta kishin ilimi.
Da yake jawabi, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar, Alhaji Sulaiman Abdullahi (aji na 1987), ya ce G.T.C Ungoggo makaranta ce da ta shahara wajen fitar da ƙwararrun ɗalibai masu amfani ga Najeriya baki ɗaya. Ya bayyana cewa makarantar ta daɗe tana buƙatar gyara, amma zuwan tallafin gwamnatin Kano ya ƙara wa tsofaffin ɗalibai ƙwarin gwiwar ƙara ba da gudunmawa domin bunƙasa ta. Ya jaddada buƙatar duk tsohon ɗalibi mai hali da kishin makarantar ya taimaka gwargwadon ikon sa.
Shi ma DPM Malam Mustapha Uba Munjibur, shugaban ma’aikata na ƙaramar hukumar Kumbotso, ya ce kishin ilimi na daga cikin manyan manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf tun farko. Ya ƙara da cewa duk wanda ya taɓa karatu a G.T.C Ungoggo shaida ne cewa makarantar ta taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwar al’umma, ba a Kano kaɗai ba har ma a faɗin ƙasar nan.
A nasa jawabin, shugaban UNTOBA aji na 1991, Aliyu Idris, ya bayyana farin cikinsa kan yadda ƙungiyar ta haɗa kan ’ya’yanta, lamarin da ya kai ga samun goyon bayan gwamnati da sauran tsofaffin ɗalibai. Ya ce wannan ci gaba abin alfahari ne kuma hujja ta cewa haɗin kai na kawo sauyi mai ɗorewa.
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr. Kabiru Muhammad Ibrahim, ya yabawa gwamnatin Kano bisa wannan gagarumin tallafi, yana mai cewa tsofaffin ɗalibai da na yanzu sun san Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin mutum mai kishin ilimi da abin da ya karanta, tare da tabbatar da cewa gwamnatin sa na tare da su wajen bunƙasa makarantar.
