AFCON 2025: Nijeriya za ta kece raini da Algeria a wasan daf da ƙarshe

Spread the love

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta haɗu da takwararta ta ƙasar Algeria a wasan zagayen daf da ƙarshe na gasar ƙasashen nahiyar Afirika da ake ci gaba da bugawa a Moroko.

Nijeriya ta kai zagayen Kwata Fainal bayan lallasa ƙasar Mozambiƙue a wasan zagayen yan 16 a ranar Litinin.

Hakazalika, Algeria ta doke Dimokuraɗiyyar Congo a wasan zagayen 16 da ci 1-0 bayan karin mintuna 30 da alƙalin wasa yayi a wasan, ƙasashen biyu za su haɗu a ranar Asabar 10 ga watan Janairu domin sanin ƙasar da zata kai matakin Semi Fainal.

Nijeriya ta samu nasara a dukkan wasanni 4 da ta buga a gasar ta bana, ta jefa ƙwallaye 12 yayin da aka zura mata ƙwallo 4 kacal a raga, a ɓangaren Algeria kuma The Desert Foxes kamar yadda ake kiransu sun zura ƙwallaye 8 a raga inda aka jefa masu ƙwallo 1 kacal a ragarsu.

By ukarofi