
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta inganta lamuran sojojin Nijeriya domin magance matsalolin harkokin tsaro da ke addabar ƙasar.
Shettima ya bada tabbacin ne a ranar Juma’a yayin gudanar da addu’o’i na musamman don girmama Ranar Sojoji da Tunawa da ‘Yan Mazan Jiya a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Ya jinjina wa sojojin da suka rasu a bakin aiki bisa sadaukarwarsu ga tsaron ƙasa da waɗanda ke aiki a yanzu da suka fifita tsaron al’umma da ƙasa akan rayukansu.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa, yana fatan Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, za ta samu zaman lafiya mai ɗorewa da nasarori nan ba da jimawa ba, yana mai yaba wa dakarun da sauran hukumomin tsaro bisa ayyukan da suke yi tuƙuru wajen daƙile ayyukan ta’addanci a sassan Nijeriya.
Gwamnatin Tarayya ta zaɓi ranar 15 ga watan Junairun kowace shekara a matsayin lokacin karrama dakarun tsaro, wadda a juya Juma’a da sauya wa suna daga ‘Armed Forces Remembrance Day’ zuwa ‘Armed Forces Celebration and Remembrance Day’ domin dacewa da ainihin ma’ana abin da ranar ta ƙunsa.





