CBN ya ja kunnen bankunan kan takura kwastomomi sakamakon sabon sharaɗin jari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗin cewa tsarin ƙara jarin bankuna da ake aiwatarwa a halin yanzu na iya jawo cunkoson masu zuba jari a kasuwar hannun jari, lamarin da ka iya kashe jikin masu saka jari tare da rage damar samun kuɗaɗe ga kamfanonin da ba na banki ba.

Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin rahoton Hasashen Tattalin Arziki na 2026 da Babban Bankin ya fitar, a daidai lokacin da bankunan Nijeriya ke hanzarta neman cika sabon sharuɗɗan mafi ƙarancin jarin aiki kafin wa’adin watan Maris na shekarar 2026.

A cewar CBN, wa’adin shekaru biyu da aka bai wa bankuna domin ƙara jarinsu, wanda aka fara aiwatarwa tun watan Maris na 2024, ya ƙara matsin lamba kan kasuwar jari, inda bankuna ke jan hankalin masu zuba jari zuwa gare su fiye da sauran sassan tattalin arziki.

Wannan yanayi, inji bankin, na iya haddasa tara kuɗaɗe a ɓangaren harkokin kuɗi kawai, tare da tauye damar kamfanoni masu zaman kansu su samu jari.

Rahoton ya nuna cewa wannan cunkoso na iya haifar da gajiyar masu zuba jari, wanda hakan zai iya raunana bunƙasar kasuwar jari baki ɗaya tare da rage bambancin masu saka jari da ake buƙata domin ɗorewar kasuwa.

CBN ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar ƙaruwa a bashin da ba a biya ba daga hannun masu karɓar rance, inda ya ce taɓarɓarewar ingancin kadarorin bankuna na iya raunana ginshiƙan kuɗinsu tare da haifar da barazana ga tsarin kuɗi na ƙasa.

Sai dai duk da waɗannan barazanar, Babban Bankin ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da daidaita tsakanin kare darajar kuɗi da kuma bunƙasar tattalin arziƙi a shekarar 2026. Bankin ya ce zai ci gaba da amfani da dabarun kuɗi da na kula da tsarin banki domin jawo jarin ƙasashen waje, daidaita kasuwar canjin kuɗaɗe da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

CBN ya ƙara da cewa haɓakar kuɗaɗen da ke yawo a tattalin arziki a shekarar 2026 za ta ta’allaƙa ne kan abubuwa da dama, ciki har da sauye-sauyen farashin canjin kuɗaɗe, harkokin kashe kuɗaɗen gwamnati, kuɗaɗen da za su shafi zaɓuɓɓuka, da kuma ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan kula da bankuna.

Masu nazarin harkokin kuɗi sun ce wannan gargaɗi daga CBN na nuna buƙatar a samu daidaito a tsarin ƙara jarin bankuna, domin kada ya zama barazana ga sauran sassan kasuwar jari. Wani masani a harkar zuba jari a Legas ya ce, duk da muhimmancin ƙarfafa bankuna ta fuskar jari, yawaitar matsin lamba kan masu saka jari na iya rage sha’awar su a kasuwa.

By ukarofi