Gwamna Lawal ya yaba wa sojoji kan jajircewarsu wajen yaƙar ‘yan ta’adda a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya yaba wa rundunar sojin 1 Brigade, wacce ke aiki a ƙarƙashin Operation FANSAN YAMMA, saboda ci gaba da sadaukarwa da jajircewarsu wajen dawo da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin bikin ayyukan jin daɗin jama’a na rundunar sojin Najeriya ta yammacin Afirka (WASA) wanda rundunar sojin Najeriya ta 1 Brigade Gusau ta shirya ranar Asabar.

Gwamnan wanda kwamishinan ayyuka na jihar Alh. Lawal Barau ya wakilta, ya sake jaddada cewa gwamnati da mutanen jihar Zamfara ba sa ɗaukar ƙoƙarin sojoji a matsayin abin wasa, yana mai nuni da cewar gwamnatin sa tana godiya da jajircewar sojojin da sadaukarwar su.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta ci gaba da haɗin gwiwa da bayar da goyon baya ga rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro, da ake da su, wajen neman zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

Yana addu’ar ci gaba da samun nasara a ayyukan su masu kyau da kuma ɗorewar zaman lafiya da wadata a jihar Zamfara da kuma Tarayyar Najeriya.

“Na gamsu da nasarar da aka samu a taron na yau, wanda ya sake nuna bambancin al’adu, haɗin kai da kuma ƙwarin gwiwar da ke bayyana rundunar sojin Najeriya ke da shi.” Gwamna Lawal ya ce.

A jawabin maraba, Kwamandan Runduna ta 1 ta Sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar M.Jimoh ya bayyana cewa bikin, ayyukan wasa ana gudanar da shi ne domin nuna al’adun alummar Nijeriya, wanda ke nuna ƙarshen ayyukan rundunar Sojin a ƙarshen shekara a hukumance.

Ya tabbatar da cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar, yana mai cewa sojoji za su ci gaba da bin diddigin ‘yan ta’adda a maɓoyarsu a jihar.

By ukarofi