
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tauraron ɗan ƙwallon ƙafa, Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo ɗaya tilo a wasan da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta sha kaye a hannun Al Hilal da ci 3 da 1, lamarin da ya jefa fatan lashe kofi na ƙungiyar a wannan kakar cikin mawuyacin hali.
Da fari Ronaldo ne ya fara zura ƙwallo a wasan, wanda daga bisani ya cabe a lokacin da Al Nassr ta jan kati ta mai tsaron gidanta.
Al Hilal ta yi nasarar ne ta ‘yan wasanta Salem Al-Dawsari, Mohamed Kanno da kuma Ruben Neves.
Wannan shi ne karo na uku a jere da Al Nassr ta ke shan kaye a wannan kakar, sannan hakan ya kai Jimmy wasanni huɗu da take rashin nasara.
Al Nassr dai ta buga wasanni 10 na farkon kakar ba tare da an doke ta a ko ɗaya ba, inda a yanzu Al Hilal da ta ɗale kan tebur ta ba ta tazarar maki bakwai akan ta su Ronaldon.
