Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yan sandan sun kama mutum uku da kayayyakin fashewa, yayin wani samamen sirri da suka gudanar a ƙaramar hukumar Daura ta jihar.
Samamen ya biyo bayan umarnin da babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun ya bayar na ƙarfafa sintiri, musamman a manyan hanyoyi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar, ya ce rundunar ta kama mutanen ne a ƙauyen Koza da ke ƙaramar hukumar.
Ya ce jami’an rundunar sun kama wata mota ƙirar Golf da wani mai suna Musa ɗan shekara 40 ke tukawa, wanda ya kai ga gano kayayyakin fashewa dubu 6,975 da aka ɓoye cikinta.
Kuma direban ya bayyana cewa ya karɓi kayayyakin fashewar ne daga wani mai suna Najib, wanda yanzu haka yan sanda na neman sa ruwa a jallo, kuma ya ɗauko su ne daga Kano zuwa Kwangolam a ƙaramar hukumar Mai’adua inda ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Bayan tsananta bincike ne ‘yan sandan suka kama wasu ƙarin mutum biyu da ake zargi, Ibrahim Murtala ɗan shekara 22 da haihuwa, da Sulaiman Muhammad ɗan shekara 35, tare da gano ƙarin kayayyakin fashewar da su ka kai 7,500 haɗe da sama da buhu 30 na kayan fashewar da nauyinsu ya kai kilogram 2,273.65.
DSP Abubakar Sadiq ya ce duka mutanen uku sun amsa cewa da hannun su a safarar kayayyakin fashewar.
Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin kama sauran waɗanda su ka tsere da ke da alaƙa da aikata laifin safarar kayan fashewar, yayin da waɗanda aka kaman da sauran an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu .
