Gwamnatin Tarayya ta ƙulla sabuwar yarjejeniya da ASUU don kawo ƙarshen rikicin shekaru 17

Spread the love

Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun rattaɓa hannu akan sabuwar yarjejeniya da nufin inganta harkokin karatun jami’o’i da tabbatar da ɗorewar al’amuransu.

Rahotanni sun bayyana cewa hakan zai taimaka wajen sauya tsarin albashi da walwalar malaman jami’o’i, tare da kawo ƙarshen dukkan matsalolin aka jima ana fuskantar su har na tsawon shekaru 17.

Yarjejeniyar ta kawo karuwar albashi da kashi 40 ga malaman jami’o’in tarayya da zai fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, tare da sabon tsarin biyan albashi da ya haɗa da CONUASS (Consolidated University Academic Staff Salary) da kuma CATA (Consolidated Academic Tools Allowance).

Wadannan gyare-gyaren an tsara su ne domin ƙarfafa bincike, ci-gaban sana’a, da kuma ƙara ƙwarewar malaman jami’o’i a mataki na duniya.

Haka kuma, an sake tsara Albashin Ayyuka Guda Tara na ‘Earned Academic Allowances’ domin daidaita biyan albashi da ayyuka kamar jagorantar digiri na biyu da na uku, aikin asibiti, jarabawa, bincike a fagen aiki, da shugabanci.

Bugu da ƙari, manyan farfesoshi da masu karatun ilimi za su samu albashi na musamman bisa ga matsayinsu da gudunmawarsu.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin “muhimmin canji” wanda zai dawo da amincewa da ƙwarin-gwiwa a tsarin jami’o’in Najeriya.

A nasu ɓangaren, jagororin ASUU sun yi maraba da yarjejeniyar a inda suka ce ta magance damuwar da ta dade tana addabar malaman jami’o’i yayin da take samar da abubuwan da za su ƙara ƙarfafa ilimi a jami’o’i.

Masana suna cewa wannan yarjejeniya za ta kawo zaman lafiya a harkar ilimi, daidaita kalandar karatu, da kuma inganta ingancin ilimi a jami’o’in ƙasar.

By Babaji