Gwamnatin Kano ta dakatar da likitoci kan barin almakashi a cikin majinyaciya har ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da asibitoci ta Jihar Kano ta ce ta tabbatar da rasuwar wata mahaifiyar ‘ya’ya biyar mai suna Aishatu Umar, lamarin da ya auku sakamakon sakacin likitoci a asibitin da take jinya, wato Abubakar Imam Urology Centre a Kano.

Haka kuma, ta tabbatar da zargin da aka yi na cewa ma’aikatan lafiyar sun bar almakashi a cikin wata matar yayin da suke mata tiyata, al’amarin da ya yi sanadin rasuwarta daga bisani.

Wata sanarwa da ta fitar na cewa Babban Sakataren Hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda ya dakatar da ma’aikatan da lamarin ya faru a lokacin aikinsu tare da gabatar da batun a gaban kwamitin ladabtarwa.

BBCHausa ta ruwaito cewa hukumar “ta dakatar da ma’aikata uku waɗanda suke da hannu a cikin lamarin nan take”.

Kazalika, sanarwar ta ce an miƙa batun ga kwamitin ladabtarwa ga ma’aikatan lafiya a jihar domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace waɗanda dokoki suka tanada.

Ta kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar kan abin bakin ciki da ya faru.

Har ila yau, tabbatar da cewa ba za ta lamunci kowane irin sakaci ba kuma za ta ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai domin kare rayuka da kuma samun amincewar marasa lafiya a faɗin cibiyoyin lafiya na Kano.

By Babaji