
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba ƙungiyar Real Madrid ta sake shiga mawuyacin hali sakamakon doke ta da Albacete da ke rukuni na biyu ta yi a gasar Copa del Rey da ci 3 da 2, wanda hakan ya haifar da rashin nasara a wasan farko na kociyanta Alvaro Arbeloa.
Wasu na ganin hakan ya faru ne a sakamakon rashin wasu daga cikin zaƙaƙuran ‘yan wasan ƙungiyar da suka haɗa da Kylian Mbappe, Jude Bellingham da Thibaut Courtois.
Akan haka ne kocin ya zuba ‘yan wasa Jorge Cestero da David Jimenez, wadsnya taɓa horar da su a baya. Saidai hakan bai sa ya yi nasara ba sakamakon zura musu ƙwallo na uku yayin da ake dab da kammala wasan.
Wannan shi ne karo na farko da Albecete ta samu nasara akan Real Madrid a tarihi, lamarin da ya ƙara dagula al’amuran Madrid tun bayan sallamar Xabi Alonso a makon da ya gabata.
Ana ganin Arbeloa a matsayin wanda zai tsamo babbar ƙungiyar daga halin ni’yasun da ta shiga na rashin nasara akai-akai a ƙarƙashin tsohon kocinta Alonso, wanda ya shafe watanni bakwai yana horar da ‘yan wasanta.
