CAF ta dakatar da Eto’o wasa huɗu da cin tarar sa kan rikici da alƙalin wasa a gaban shugabanta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Afirka (CAF) ta yi hukunci akan Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Kamaru (FECAFOOT), Samuel Eto’o akan nuna rashin ladabi yayin wasan kusa da na dab da na ƙarshe da ƙasarsa ta sha kaye a hannun Moroko a gasar kofin ƙasashen Afirka, AFCON.

A sanarwar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Alhamis, kwamitin ladabtarwar CAF ya tabbatar da cewa an ɗauki matakin akan Eto’o ne sakamakon rashin biyayya da karya dokokin wasanni na Sashe na 2(3) na hukumar.

A cewarta, an samu tsohon ɗan wasan na Barcelona da Inter Milan da laifin rashin ladabi ga dokokin wasanni a lokacin wasan, wanda Moroko ta doke Kamaru da ci 2 da nema.

An ruwaito cewa Eto’o ya nuna rashin ɗa’a ga hukunce-hukuncen alƙalan wasa akan idon shugaban CAF, Patrice Motsepe.

Akan haka ne kwamitin ladabtarwar ya dakatar da Eto’o na tsawon wasanni huɗu da cin sa tarar Dala 20,000.

Moroko mai masauƙin baƙi za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe, yayin da Nijeriya da ta sha kaye a hannunta a wasan dab da na ƙarshe, za ta kara da Masar a wasan neman gurbi na uku a ranar Asabar.

By Babaji