
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar ADP ta miƙa saƙonta na gaisuwa da taya murna ga Rundunar Sojin Nijeriya a bisa zagayowar ranar tunawa da ‘yan mazan jiya.
ADP, wato ‘Action Democratic Party’, a wata takarda da ta fitar ta hannun Shugabanta, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ta tunatar da jarumta sadaukarwa da hidimta wa ƙasa ba tare da gajiyawa ba ga Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya da dakarun tsaron ke yi don al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana karamcinta ga jami’am rundunar maza da mata da suka rasa rayukansu wajen kare haɗin kan ƙasa, iko da tsarin mulkinta, tana mai yaba wa sadaukarwarsu da ta zama ginshikin samun ‘yancin al’ummar ƙasar.
Ta ƙara da cewa: “muna yaba wa dakarunmu da ke kan aiki a halin yanzu, waɗanda duk da tsananin kalubalen aiki ke ci gaba da fuskantar ta’addanci, ‘yan bindiga, sace-sace, da sauran barazanar tsaro a fadin kasa. Rundunar Sojin Nijeriya ta dauki nauyi mai girma a shekarun baya-bayan nan—ta yin aiki a fannoni da dama na tsaro tare da daidaita dabaru da sabbin nau’o’in barazana. Juriya da kwarewarsu sun cancanci godiya daga dukkan ‘yan Nijeriya.”
Kazalika ADP ta fahimci cewa matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a yau ba laifin rundunar soji ba ce, illa sakamakon abin da ta kira da “dogon giɓi a harkokin shugabanci, matsalolin tattalin arziƙi, sauyin yanayi, da kuma lalacewar yankunan da gwamnati ba ta da cikakken iko a kansu”.
“muna kira da a daidaita sadaukarwar dakarunmu, ayyukan tsaro na zamani da ke dogaro da bayanan sirri, ingantaccen walwala da kulawa ga dakarunmu tare da bin doka da oda, gaggauta tabbatar da tsaro bayan kammala hare-hare ta hanyar ‘yan sanda, shari’a, da hanyoyin samun abin yi, da tsarin haɗin-gwiwar dukkan ɓangarorin gwamnati domin sauya nasarorin fagen fama zuwa tabbataccen tsaron fararen hula”, inji ta.
Har ila yau, ADP ta jaddada kudirinta na goyon bayan manufofi da ke karfafa tsaron kasa, kare rayukan fararen hula, da dawo da cikakken ikon gwamnati a kowace al’umma, tana mai yi wa jami’an da suka rasu addu’ar samu rahama da taimakon ubangiji ga waɗanda ke raye.
