
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wani jagoran harkar dillancin ƙwaya da aka daɗe ana nema ruwa-a-jallo mai suna Lekan Jimoh da aka sani da “Kanmo-Kanmo”.
An yi nasarar haka ne bayan shekaru 12 da ake zargin sa da hannu a kisan wasu jami’an hukumar guda uku.
A ranar Juma’a, 16 ga watan Junairu, 2026 aka kama Jimoh a garin Owode da ke Jihar Ogun bayan wani atisayen sirri da aka gudanar ƙarƙashin tawagar ayyukan na musamman ta hukumar.
Haka kuma, a yayin bincike a maɓoyarsa, an gano kilogram 69 a tabar ‘skunk’.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi a wata sanarwa, ya ce tun a ranar 15 ga watan Yunin 20214 aka sanya sunan wanda ake zargin a sahun waɗanda ake neman ruwa-a-jallo, wanda a lokacin ne ya shirya wasu ɓata-gari suka kai wa jami’an NDLEA hari yayin da suka yi yunƙurin kama shi a maɓoyarsa.
Ya ce, kamen kasurgumin dillalin wata babbar nasara ce ga ƙoƙarin hukumar na tabbatar da babu wani tantiri da ya gagari doka ta riske shi ko da kuwa an ɗauki tsawon lokaci ana neman sa.
A ranar da al’amarin ya faru, miyagun sun halaka jamai uku ciki har da Rabi’u Usman Kazaure, inda yunƙurin kama su Jimoh da ya jagoranci tawagar bai kai ga nasara ba.
