Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar aiki fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda yanzu haka yake ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi ci gaban Jihar Kano, haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jiha, da wasu muhimman al’amuran ƙasa da suka shafi jin daɗin al’umma.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa ganawar na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar aiki tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya domin samar da ci gaba mai ɗorewa a Arewa da ƙasar baki ɗaya.
Sannan akwai batun nan na sauya shekar gwamna zuwa Jam’iyyar APC batun da ke ta da hazo a siyasar Kano da ƙasa baki ɗaya.
