Jami’an DSS sun sake kama Malami jim kaɗan bayan sako shi daga kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Matsalolin shari’a da siyasar tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) sun yi ƙamari yayin da a ranar Asabar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka sake yin ram da shi jim kaɗan bayan sako shi daga gidan yari na Kuje da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da Malami ofishin hukumar ne bayan cika sharuɗɗan belin da kotu ta ɗora masa a lokacin da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta kama shi bisa zargin sa da hannu a badaƙalar kuɗaɗe.

A kwanakin baya ne EFCC ta kama Malami da matarsa da ɗansa bayan faɗaɗa bincike akan zargin badaƙalar. Daga bisani kotu ta bada belinsu akan Naira miliyan 500 ga kowane ɗaya daga cikinsu da ƙarin wasu sharuɗɗa da suka jinkirta sako su.

Bayan cika sharuɗɗan da ficewa daga kurkukun, nan da nan jami’an na DSS suka kama shi a wani yanayi da majiyoyi suka bayyana a matsayin “shiryayyen aiki tsakanin hukumomi”.

Majiyoyin tsaron sun bayyana cewa kamen na DSS ya biyo bayan bayyanar ƙorafe-ƙorafe da dama da ke zargin sa da hannu a ɗaukar nauyin ta’addanci, laifin da ake ɗauka a matsayin mafi girma acikin laifukan tsaron ƙasa da ƙasa-da-ƙasa.

A cewar wata majiya mai kusanci da binciken, DSS ta shigo cikin al’amarin ne bayan EFCC ta gano wasu muggan makamai a gidan Malami a Jihar Kebbi yayin binciken da ta gudanar akansa.

Saidai duk da haka, Malami na cigaba da musanta dukkan zarge-zargen da ake yi akansa inda ya bayyana hakan a matsayin abin da siyasa ta shigo ciki, yana mai tirjewa akan ba shi da hannu a dukkan abin da ake tuhumar sa a kansu.

By Babaji