Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
A ranar 15 ga watan Janairu 1966 mugayen mutane a sojoji karkashin jagaorancin ‘yan kabilar Igbo su ka aiwatar da juyin mulki na farko a Nijeriya da zubar da jinin shugabannin al’umma abun alfahari. Shekaru 60 kenan bana da aikata wannan ta’addanci na kisan gilla ga Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto Gamji mazan kwarai, Firaministan Nijeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan kudu maso yamma a babban birnin Badun Chirf Ladoke Akintola. Haƙiƙa Gamji ya na nan daram a zukatan al’ummarsa inda makiya Arewa har yau ke ci gaba da neman murde wuyan tarihi don nemawa masu kisan gilla uzuri ko dalilin zubar da jinin waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba.
Babban maciyin amana shi ne Chukwuma Nzeogwu Kaduna wanda ya samu duk gatan da ya ke bukata daga wajen Gamji amma shi ne ya ɗau bindiga ya harbe Sardauna inda a nan matarsa Hafsa ma ta yi shahada a hannun wannan mugun mutumin mai cutar kabilanci da kafurci. Hakika Sir Ahmadu Bello ya na da labarin shirin zubar da jininsa kuma an ma nemi ya bar ƙasar don gujewa mugun lamarin da zai iya aukuwa, amma ina imaninsa na ganin ai al’umma ta ba shi amana ta jagoranci don haka ba zai tafi ya bar al’umma ba sai bayan ransa! Shin zuwa yau akwai jagora da zai samu labarin an shirya shekar da jininsa ya kuma zauna? Yo ciwon kai ma ya ke fitar da jagorori ƙetare balle a je ga maganar yiwuwar fuskantar bakin bindiga.
Bayan shekara 1 da kimanin wata 6 da kwana 15 shi ma Nzeogwu da a ka ƙarawa girma zuwa Laftanar Kanar a sojan ‘yan awaren Biyafara ya gamu da gamonsa na tafiya lahira ba shiri a daf da Nsukka yayin tozali da bataliya ta sojan tarayya ta 21 karkashin Kaftin Muhammad Inuwa Wushishi. Hatta shi kansa Aguiyi Ironsi da ya haye madafun iko bai zauna kan karaga fiye da wata 6 da kwana 15 ba ya tafi lahira ba shiri. Miyagun da su ka zubar da jinin Gamji da sauran shugabannin da su ka tsana a jamhuriya ta farko ba su samu yin dabdalar da su ke hasashe ba don kasa ta haɗiye su kuma ba su bar wani tarihi mai kyau ba don duk ranar da za a tuna su, sai an kawo batun ta’addancin ranar 15 ga Janairu 1966.
Laifin Gamji da ya cancanci kisan gilla ƙarfafa ‘yan arewa su jagoranci yankinsu:
Babban abun da ya zama laifin Gamji wajen miyagun iri ‘yan kabilanci su Nzoegwu shi ne ƙarfafa guiwar ‘yan Arewa su taso su rike madafun ikon Lardinsu kamar yadda sauran Larduna su ke yi. Gamji bai amince a yi gaggawar mika ’yanci ga Nijeriya ba, sai da ya tabbatar an samu aƙalla masu ilimi ‘yan Arewa da za su iya gogayya da sauran ’yan bokon sauran Larduna. Haƙiƙa su Nzeogwu sun so yi wa Arewa mulkin mallaka karo na biyu ne wato bayan tafiyar jan Bature su zama ‘yan mulkin mallaka na bakaken Turawa. Cikin ikon Allah Gamji a ɗan takadirin lokacin da ya samu na jagoranci ya kafa gagarumar jami’a ta ABU a Zaria da har gobe ta ke zama abun alfahari. Ya kafa cibiyoyin kuɗi, ingantaccen tsarin samun ilimi, zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da ƙabilu mabambanta. Don matuƙar rashin nuna wariyar Gamji, ya zama babban likitansa Dokta Ishaya Audu kirista ne daga karɓar addinin na Kirista tun kan mahaifinsa Mr.Bulus Audu mutumin Anchau a ƙasar Zazzau. Zama lafiya da Sarkin Kagoro Gwamna Awan wanda babban Sarki ne mabiyin addinin kirista daga Kudancin Kaduna na nuna karin shaidar ɗaukar al’ummarsa ba tare da bambanci ba. Ga irin shaida ta zama lafiya da Chief Micheal Audu Buba daga jihar Filato. Misalai ne na adalcin Sardauna da ba a taba gani ba a tsakanin jagororin Nijeriya.
Mabiya siyasar hamayya ta NEPU da ke adawa da NPC ta Sardauna sun so yin murna lokacin da a ka yi wa Gamji kisan gilla amma jagora Malam Aminu ya taka mu su birki da nuna mu su ai siyasa ba ƙiyayya ba ce kuma ai ba su da irin mutum babban jagora nagari da ya sha gaban Gamji.
BABBAN DARASI DAGA RAYUWAR SARDAUNA
Gaba da baya Gamji shekaru 56 ya yi a duniya amma yau an maimaita shekarunsa na rayuwa bayan mutuwarsa an ƙara har da 4 amma kamar jiya a ka yi kisan gillar don in ka shiga Kaduna za ka ga kamar ka na tare da Gamji, in ka leƙa jami’ar Ahmadu Bello ka ga shingenta ya doshi Funtua za ka zubar da hawaye ga kishin ƙasa irin na Gamji a ce wasu tunaninsu su shekar da jininsa. Bai bar azurfa ba balle zinari amma ya bar ayyukan alheri bila-adadin da a ke tuna shi da su a yi ma sa addu’ar rahama. Miyagun da su ka yi ma sa kisan gilla su ma ba sa doron duniyar in ka ɗebe wasu ‘yan barandarsu da su ka gaji kiyayya ga mutanen kirki.
Akwai buƙatar ‘yan Arewa su farka su yi bitar ayyukan raya kasa na sadaukar da kai na Gamji don yin koyi da shi. Ya zama wajibi ‘yan Arewa su farka su yaƙi makiya Arewa masu son ganin sun kunna fitinar yaƙin ƙabilanci don kammala mugun muradin waɗanda su ka zubar da jinin Gamji amma su ka koma Lardinsu don tawaye ga kasa mai ‘yanci. Kamar yadda da alamu maƙiya ba za su ajiye makaman sharri ba, hakanan al’ummar Arewa su yi tsayin daka su kare yankinsu ta karfafa ‘yan uwantaka da tarihi na gaskiya.
Duk mai aibata Sardauna dillalin miyagun can ne masu kisan gilla kuma haƙarsu ba za ta taba tadda ruwa ba don ba su da manufa mai kyau da ta wuce haddasa ƙiyayya da zama cikin ruɗani. Da yadar Allah ba wanda ya isa ya mayarda Arewa zuwa yanayin zamanin jahiliyya. Gamji ya kafa makarntu mutane sun samu ilimi na addini da zamani. Tsakaninmu da magabata irin Gamji sai addu’ar alheri. Allah ya jiƙan mazan kwarai.
Bayan kisan gilla ga Sardauna akwai jami’an da su ka buya don gudun zaluncin rundunar Nzeogwu. Marigayi ministan Ilimi Wazirin Katsina Alhaji Isa Kaita ya shaidawa Sheikh Abubakar Gumi labarin juyin mulkin da sojoji su ka yi kuma ya buƙaci ya tafi gidan Firimiya don duba abun da ya wakana. Nan Sheikh Gumi ya yi sallar asuba ya kuma kama hanya sai gidan Arewa ya tarar da ko ina ya turnuƙe da hayaƙi don an yi amfani da manyan makamai wajen farmakin, ga sojoji nan da can riƙe da bindigogi, ya kutsa kai cikin gidan ya tarar da gawar Sardauna cikin jini a nan inda a ke tsayar da motoci. An kashe Sardauna da matarsa Hafsa. Nan Sheikh Gumi ya ce a kai marigayan gidan sarkin musulmi a nan anguwar Sarki inda a ka shirya su kuma Sheikh ya yi mu su sallar jana’iza. Allahu Akbar Sheikh Gumi jan gwarzo ne da masu kisan gilla ba su sa ya raurawa ba.
A ranar aiki, Sheikh Gumi na ofishinsa sai Nzeogwu ya turo sojoji su ka dauke shi zuwa wajensa. Nan ya tari Sardauna cikin murmushin jin daɗin ya kashe Sardauna. Nan ya tambayi Sheikh Gumi inda su ka kai makaman da su ka shigo da su daga ƙetare don yin jihadi. Sheikh Gumi cikin al’ajabi don ya yi tsammanin ko Nzeogwu zai yi ma sa ta’aziyya ne duk da dama ba ya tsammanin nadama daga wajen mugun maciyin amana dan ruruta yakin ƙabilanci. Sheikh Gumi ya nemi ƙarin bayanin abun da Nzeogwu ke nufi. Nan Nzeogwu ya ce sun samu labarin Sardauna ya shigo da makamai daga kasashen Larabawa don yaƙi da duk waɗanda ba Musulmi ba ta hanyar kaddamar da jihadi. Nan Sheikh Gumi ya ce ma sa a wajensa ya fara jin labarin nan kuma duk ziyarar Sardauna kasashen Larabawa tare su ke tafiya a matsayinsa na mai ba shi shawara kan lamuran Musulunci kuma ba inda a ka taɓa irin wannan mummunar magana watsatstsiya.
A nan Sheikh Gumi ya fahimci ƙirƙire-ƙirƙiren karya na zargin musulmi za su kai wa wadanda ba Musulmi ba hari, su ka haddasa kisan gilla ga Sardauna. Haƙiƙa daya dalilin na zahiri shi ne fifita al’ummar Arewa da Gamji ya yi don karfafa su, su ilmantu da kula da Lardinsu don kar su zama ‘yan kallo a ƙasa. Har yau wannan alherin na Sardauna duk ‘yan Arewa ke amfana da shi ciki kuwa har da ‘yan barandan IPOB masu son kunna wutar fitina a Arewa don hakan ya ba da damar kafa Biyafara da ƙasar ƙabilanci ta MIDDLE BELT. Manjo Gideon Orkar ya so farfado da wannan mummunar ƙiyayya ta karya lokacin da ya yi yunƙurin kifar da gwamnatin Janar Babangida a 1992 ya kori jihohin da ba na iƙirarin yankin MIDDLE BELT ba daga Najeriya. Su Orkar sun yi nasarar zubar da jinin dogarin Janar Babanbida wato Laftanar Kanar UK Bello.
KAMMALAWA
Duk makiyin Shehu Mujaddadi na kammala aikin Turawan mulkin mallaka ne na yaƙi da tasirin Musulunci. Sammakal ne makiya Sardauna na koyi ne da karyar da Nzeogwu ya hau kan ta wai Sardauna ya shigo da makamai daga kasashen Larabawa don yaƙi da waɗanda ba Musulmi ba wai Sardauna zai yi jihadi!.
Miyagun iri ba za ku yi nasara ba, Turawa sun gwada har da datse kan Sultan Attahiru sun gaza. Nzeogwu ya harbe Sardauna bisa doron karya ya gaza. Gideon Orkar ya kori jihohin waɗanda ya tsana daga Nijeriya amma juyin mulkinsa ya juye kansa. Nnamdi Kanu ya yi ta zagin Nijeriya da zayyana ta da gandun adana dabbobin daji amma yau ya na gidan yari. Yo dakkan shaidanu ma ba su cimma buri ba balle tarkace ‘yan baranda masu buya a wayar salula ba hoto ba sunan gaskiya.
