Zargin ɗaukar nauyin ta’addanci: Kotu ta bada belin Kwamishinan Kuɗin Bauchi akan miliyan N100

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da belin Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu da wasu mutane uku da aka shigar da su ƙara tare akan Naira miliyan 100 ga kowannensu na zargin ɗaukar nauyin ta’addancin Dala miliyan 9.7.

Haka kuma alƙalin ya umarci su Adamu da gabatar da mutane biyu-biyu da za su tsaya musu masu muƙaman babban sakatare ko darakta a aikin gwamnati.

Sannan, ya umarci da a saki Yakubu har zuwa ranar 26 ga watan Fabarairu, 2026, inda za a cigaba da sauraron ƙarar da ake tuhumarsu a kai.

Da fari, an tsare kwamishinan ne tare da mutane ukun bisa zargin su da hannu a badaƙalar kimanin Dala miliyan 9.7 da ya yi amfani da shi wajen rura wutar ta’addanci a jihar Bauchi.

Baya ga karɓe takardar fasfo ɗinsa, kwamishinan zai riƙa zuwa ofishin Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke Bauchi a kowace Litinin har zuwa ranar sauraron shari’ar.

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati ta shigar da tuhume-tuhume guda goma masu alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci da badaƙalar kuɗaɗe a kotu akan Adamu da sauran ukun.

By Babaji