
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin manyan jami’an Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ya yi ƙorafin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a wajen Shugaba Bola Tinubu na neman ya tsige shi daga shugabancin hukumar.
Kwamishinonin sun zargi shugaban, wanda aka fi sani da Abdullahi Pakistan da hannu a rashawa, rashin ƙwarewa da wulaƙanta aiki acikin takardar ƙorafin nasu.
Saidai, a wata hira da jaridar Daily Trust, Farfesa Abdullahi Saleh ya ce galibin ƙorafe-ƙorafen cikin hukumar sun samo asali ne daga fushi daga wasu na an tafi Saudiyya da wasu jami’ai su kuma an bar su ko kuma wani ya samu wani abin da wasu ba su samu ba.
A ranar 19 ga watan Junairu, 2026 aka fitar da rahoton, mai taken “Vote of No Confidence in the Chairman of the National Hajj Commissioner of Nigeria (NAHCON), Prof. Abdullahi Saleh Usman”, wanda ke ɗauke da sanya hannayen: Farfesa Abubakar A. Yagawal, Prince Anofi Elegushi, Prince Aliu, Farfesa Muhammad Umaru Ndagi, Alhaji Abba Jato Kala, Sheikh Muhammad Bin Uthman, Dakta Tajudeen Abefe Oladejo, Hajia Aishat Obi Ahmed, Hajia Zainab Musa, Farfesa Musa Inuwa Fodio da kuma Farfesa Mahfouz A. Adedimeji.
Mambobin tawagar sun bayyana cewa, sun ɗauki matakin ne bayan dogon nazari akan harkokin cikin gida na hukumar bayan tsawon lokaci suna ƙoƙarin gyara game da salon jagorancin nasa, amma abin ya gagara, wanda a cewarsu, hakan barazana ce ga gaskiya da ɗorewa da kuma ƙwarewar ayyukan NAHCON.
Sun kuma zargi shugaban da rashin ƙwarewa wajen gudanar da kuɗaɗen hukumar, wanda ya saɓa wa tsare-tsare da dokokin kula da kuɗaɗen al’umma da NAHCON ta gindaya.
Haka kuma, sun yi ikirarin an sha kashe kuɗaɗe a ƙarƙashin ikonsa ba tare da neman amincewar kwamitin ba gami da bayar da kwangiloli na sama da iyakar kasafin da aka yi.
Yunƙurin ji ta bakin mai taimaka wa shugaban akan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Mu’azu a yayin haɗa wannan rahoton don ƙarin haske ya ci tura.
