
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da tura jakadu guda huɗu zuwa ƙasashen Amurka, Birtaniya, Faransa da kuma Turkiyya, wanda shi ne rukunin farko na jakadun da ak tura tun bayan tabbatar da su da Majalisar Dattawa ta yi a shekarar da ta gabata.
Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da haka wata takarda, ranar Alhamis, inda ya ce waɗanda sune sahun farko daga cikin guda 69 da Majalisar ta tantance a watan Disamba.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ya amince da tura Ambasada Ayodele Oke a matsayin jakadan Nijeriya zuwa ƙasar Faransa, yayin da Kanal Lateef Are zai wakilci Nijeriya a Amurka.
Haka kuma, an amince da tura Ambasada Aminu Ɗalhatu, wanda tsohon jakadan Nijeriya ne a ƙasar Koriya ta Kudu, a matsayin Babban Kwamishina zuwa Birtaniya.
Sai na huɗunsu, wato Sa’idu Usman Ɗakingari, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, a matsayin wanda zai wakilci Nijeriya a Turkiyya.
Tuni shugaban ƙasar ya bada umarni acikin wata wasiƙa da ya aike wa Ma’aikatar Harkokin Waje da a sanar da gwamnatocin ƙasashen da abin ya shafa, bisa ka’idojin hulɗar difulomasiyya.
Da fari Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen waɗanda yake neman naɗa su jakadu su guda 65, waɗanda daga ciki akwai 34 da suke da ƙwarewa a fannin da kuma 31 da ba su da ƙwarewa a fannin da kwamishinoni.
