Abin da ya faru da Ojo Kingsley ya yi kama da labarin fim mai cike da al’ajabi. A rana guda, kuskuren tsarin banki ya sauya rayuwarsa gaba ɗaya, inda First Bank ta tura masa sama da naira biliyan 1.3 bisa kuskure. Maimakon ya sanar da bankin ko ya mayar da kuɗin, Kingsley ya ɗauki matakin da ya jefa shi cikin mummunar masifa.
Bayan samun kuɗin, nan take ya rarraba wani kaso mai yawa zuwa asusun mahaifiyarsa, Itohan Ojo, da kuma ‘yar uwarsa, Edith Okoro Osaretin. Bai tsaya nan ba, ya kuma kashe wani ɓangare wajen kammala ginin gidansa, sannan ya soma rayuwar alfarma da nuna isa – motoci, shagali da walwala suka fara bayyana a rayuwarsa cikin ƙanƙanin lokaci.
Sai dai wannan “arziki” na bazata bai daɗe da shi ba. Hukumar EFCC ta cafke shi bayan First Bank ya shigar da ƙorafi, tana bayyana cewa kuskuren tsarin kwamfuta ne ya jawo tura masa kuɗin da ba nasa ba. Binciken EFCC ya gano yadda Kingsley ya rarraba kuɗin ga ‘yan uwansa tare da yadda ya kashe wani kaso a ayyukan kansa.
A sakamakon binciken, EFCC ta samu nasarar ƙwato naira 802,420,000 daga asusun da aka gano. A ranar Talata a Abuja, kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya bayyana cewa kuɗin da aka kwato an miƙa su ga First Bank a hukumance.
Muƙaddashin Daraktan EFCC na shiyyar Benin, Sa’ad Hanafi Sa’ad, shi ne ya miƙa kuɗin a matsayin takardar biyan kuɗi ga wakilan bankin.
A jawabinsa, Sa’ad ya jaddada cewa dokar kafa EFCC ta ba su damar bibiyar dukiyar da aka samu ta haramtacciyar hanya tare da mayar da ita ga waɗanda abin ya shafa.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da tabbatar da cewa masu aikata laifukan kuɗi ba za su amfana da laifinsu ba, domin a toshe hanyoyin aikata irin waɗannan laifuka tun daga tushe.
A nasa ɓangaren, Olalere Ajayi, Manajan Kasuwanci na First Bank a Benin, wanda ya karɓi kuɗin a madadin bankin, ya yaba wa EFCC bisa saurin aiki da ƙwarewar da ta nuna wajen gudanar da binciken. Ya bayyana hukumar a matsayin ɗaya daga cikin hukumomin Nijeriya mafi inganci da abin dogaro.
Rahoton ya ƙara da cewa, Kingsley tare da sauran waɗanda ake zargi a lamarin an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin satar kuɗi.
Wannan lamari ya zama darasi mai ƙarfi ga duk wanda ke tunanin amfana da kuskuren wasu, domin arzikin da bai dace ba kan iya zama silar faɗawa cikin bala’i.
