
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire na Jihar Kano, Yusuf Ƙofar Mata ya ajiye muƙaminsa na kwamishina, inda ya ce matakin ya biyo bayan sauye-sauyen siyasa da suka kauce wa tsarin da aka gina gwamnatin a kansa.
Yusuf Ƙofar Mata ya sanar da hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya ce ya yanke shawarar ne domin bin ƙa’ida da akidar siyasar da aka kafa gwamnatin Kano mai ci a kai.

Ya kuma nuna godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki, sannan ya miƙa godiya ta musamman ga jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rai’u Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa damar da suka ba shi na yi wa al’umma hidima.
Kazalika, ya gode wa al’ummar jihar bisa goyon baya da haɗin kai da suka nuna masa a lokacin da yake gudanar da ayyukansa a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, tare da sauran muhimman ayyuka da ya ce sun taimaka wajen ciyar da jihar gaba.
A wani labarin kuwa, wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa Mustapha Rabi’u Musa, wanda ɗan tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne, ya bayyana aniyarsa ta neman sauka daga muƙamin Kwamishinan Ci-gaban Matasa da Wasannin.
A cewar majiyar, Mustapha ya sanar da mahaifinsa batun shirin nasa, inda jagoran na NNPP ya shawarce shi da ya cigaba da zama a muƙamin domin hidimta wa al’umma ba don wata maslaha ta gwamnan ba.
Saidai, majiyar ta ce duk da wannan shawara ta mahaifin nasa, Mustaphan ya cigaba da tirjewa akan ajiye aikin. A yanzu haka dai ana sa ran ya fitar da takardar sauka daga muƙamin a hukumance.
