
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Oyo, ta ce jami’anta sun ti nasarar kama wata tirela mai maƙare da ababen fashewa a yankin Saki da ke jihar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’arta, DSP Olayinka Ayanlade ya fitar, an cafke motar ne a wani shigen bincike yayin da jami’an suke bakin aiki.
Ya ce, tuni aka garzaya da motar da ababen fashewar zuwa ofishin jami’an, waɗanda ake cigaba da gudanar da bincike akansu.
Jami’in ya ƙara da cewa an yi nasarar kamen ne sakamakon samun wani bayani na sirri, inda bayan haka ne sai Kwamishinan ‘yan sandan jihar Femi Haruna ya umarci a gaggauta ƙaddamar da bincike akan al’amarin.
Daga nan ne aka tura jami’an sashen al’amuran ababen fashewa (EOD) da na sinadarai (CBRN) domin tattara ababen yadda ya dace da yin nazari akansu, wanda tuni aka fara.
Tuni aka kao direban babbar motar zuwa ofishin rundunar, wanda kuma yake bada haɗin kan da ake buƙata ga masu bincike domin samun cikakken bayani akan al’amarin.
