An maye gurbin tutocin NNPP da na APC a gidan gwamnatin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidan gwamnatin jihar Kano ya ɗauki sabon salon siyasa yayin da aka cire tutocin jam’iyyar NNPP tare da maye gurabensu da na APC mai mulki, lamarin da ke nuna an samu sabon sauyi a karon farko tun bayan kama mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin tarbar gwamna zuwa cikin jam’iyyar APC a hukumance a yau Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa an kawata harabar gidan gwamnatin da launuka da tutocin APC, lamarin da ya ƙara jawo hankalin jama’a gabanin taron da za a gudanar domin sanar da sauyin.

Tuni tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya isa Kano domin tarbar gwamnan wanda ke nuna alamar sulhu da haɗin kai a APC.

Ana sa ran gwamnan zai sanar da komawarsa APC tare da ƙaddamar da rajistar mambobi ta intanet.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi da dama za su bi gwamnan APC, lamarin da ka iya sauya taswirar siyasar Kano baki ɗaya, yayin da aka ƙara tsaurara tsaro a wuraren da abin ya shafa.

By Babaji