
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Anambara, Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya umarci a gaggauta rufe kasuwar Onitsha na tsawon mako guda sakamakon saɓa wa dokar gwamnati daga ɓangaren ƙananan ‘yan kasuwa ta a riƙa fara hada-hadar kasuwanci a ranakun Litinin.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne a yau Litinin yayin ziyarar gani da ido a kasuwar tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa bayan gano da dama daga cikin shagunan kasuwar a rufe suke bisa haramtaccen umarnin zama a gida na ƙungiyar IPOB.
Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin abin da ya zama wajibi domin farfaɗo da daidaiton al’amuran kasuwanci da cire wa ‘yan kasuwa tsoron da ya yi sanadiyyar rushewar martabar harkokin kasuwanci a Kudu maso Gabas.
A cewar Soludo, duk da cewa gwamnatin ta sha bada tabbacin inganta tsaro da magiya ga ‘yan kasuwa da su koma aiki, har yanzu ‘yan kasuwa da yawa ba sa zuwa kasuwar, lamarin da ya zama barazana ga ɗaya daga cikin cibiyoyin kasuwanci a yammacin Afirka.
Ya kuma yi gargaɗin akwai yiwuwar a ƙara wa’adin rufewar matuƙar ‘yan kasuwar suka ƙi buɗe shagunansu bayan mako guda, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙaddamar hukunci akan waɗanda suka saɓa wa umarninta.
Akan haka ne, gwamnatin ta samar da tsarin bada albashi ga ma’aikatanta bisa la’akari da zuwansu aiki a matsayin wata hanya ta daƙile zaman gidan.
