Daga ƙarshe, Rundunar soji ta tabbatar da kitsa hamɓarar da gwamnatin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar sojoji ta tabbatar a hukumance cewa wasu daga cikin jami’anta sun shirya makircin kifar da gwamnatin Shugaban Bola Tinubu, lamarin da ya kawo ƙarshe jita-jitar tsawon watanni akan batun.

A watan Oktoban 2025, aka samu rahotannin cewa sashen leƙen asiri na sojoji (DIA) ya kama wasu jami’an soji masu muƙamin kyaftin zuwa birgediya janar tare da tsare su saboda zargin su da yunƙurin hambarar da gwamnatin Tinubu.

A wata sanarwa da ya fitar bayan rahoton a yau Litinin, Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-Janar Samaila Uba, ya tabbatar da cewa kwamitin binciken ya miƙa rahotonsa ga hukumar da ta dace.

Ya bayyana cewa, za a gurfanar da waɗanda aka samu da laifin a gaban kwamitin shari’a na sojoji domin su fuskanci hukuncin shari’a kamar yadda dokar rundunar soji da sauran ka’idojin hidimar ƙasa suka tanada.

Ya ce, “Rundunar Sojin Najeriya (AFN) na son sanar da jama’a cewa an kammala bincike kan lamarin kuma an mika rahoton ga hukumomin da suka dace.

Kazalika, tsarin binciken da aka gudanar bisa ka’idojin soji da aka kafa, ya yi nazari sosai akan al’amarin duk wani yanayi da ya dabaibaye ma’aikatan da abin ya shafa.

By Babaji