Jihar Katsina za ta wakilci Arewa maso Yamma a gasar ƙwallon kwando ta ƙasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya na Jihar Katsina (SUBEB) Dr. Kabir Magaji Gafiya ya bayyana hakan, lokacin da yake karrama tawagar ɗaliban da suka wakilci Jihar Katsina, bayan da suka zo na biyu a gasar ƙwallon kwando naJihohin Arewa maso Yamma da ya gudana a garin Dutse, Jihar Jigawa.

A lokacin da yake jawabi a lokacin da ya ƙarɓi tawagar yan wasan a Ofishin.

Dr. Kabir Magaji Gafiya ya yabawa tawagar ɗaliban tare da malaman su, akan gagarumar nasarar da suka samar wa Jihar Katsina a yayin wannan gasa.

Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa na cigaba da tallafawa harkokin wasannin motsa jiki ga ɗaliban makarantun firamare, Dr. Kabir Gafiya ya kuma bayyana irin rawar da ɗaliban Jihar ke takawa a dukkanin gasar da ake shirya wa a matakin Jihohi, da ƙasa, dama duniya baki ɗaya.

Kazalika, ya yabawa shugabannin da suka jagoranci tawagar ƙarkashin jagorancin shugaban sashen kula da harkokin wasanni a hukumar (SUBEB) Alhaji Nura Garba, inda ya bada tabbacin cigaba da ƙarfafa wa tawagar guiwa, domin samun nasara a babbar gasa ta ƙasa da za a gudanar inda ɗaliban Jihar za su wakilci Jihohin shiyar Arewa maso yammacin Nijeriya.

A jawabinsa shugaban tawagar kuma daraktan Sashen harkokin ilimi na hukumar SUBEB Alhaji Bishir Ahmad Mani ke ya sanar tawagar ɗaliban da samu nasarar wakilcin Jihohin Arewa maso Yamma, a matakin a wasan ƙasa da za a gudanar a Jihar Bauchi, a makon farko na watan Fabrairu 2026.

Daga bisani, sai ya godewa shugabancin hukumar SUBEB, akan samar da duk kayayyakin da suka kamata, tare da ɗaukar nauyin tawagar a matakin gasar jihohi da aka gudanar a Jihar Jigawa.

By ukarofi