Daga RABI’U SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta jinjinawa mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da Uwargidansa, Hajiya Nana Kashim Shettima, bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen tallafawa mahaddata Alƙur’ani.
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne yayin bikin karrama mahaddata Alƙur’ani da suka wakilci ƙasa a wata gasa ta ƙasa da ƙasa, inda ya ce irin wannan tallafi na ƙarfafa addini da ilimi abin a yaba ne kuma ya dace shugabanni su yi koyi da shi.
A yayin taron, gwamnan ya sanar da cewa za a ɗauki nauyin cigaba da karatun Hafsat Muhammad Sada, wadda ta zo ta farko a gasar kuma ‘yar ƙaramar hukumar Nasarawa ce a Jihar Kano, a ɗaya daga cikin ƙasashen Saudiyya ko Misira.
Haka kuma, gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin tafiyarta zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Kazalika, gwamnan ya gwangwaje sauran waɗanda suka yi nasara a gasar da kuɗaɗe da kuma raba filaye domin ƙara zaburar da sauran al’umma, musamman matasa, su rungumi haddar Alƙur’ani da neman ilimin addini.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Umar Tasiu da ya zo na biyu, da Sadiya Abubakar da ta zo na uku, tare da wasu mutane huɗu da suma suka amfana da kyautar filaye da kuɗaɗe.
Gwamnatin Jihar Kano ta kuma miƙa sakon godiya ga shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Ambasada Yusuf Imam Ogan Boye, bisa gudunmawar da ƙaramar hukumar ta bayar wajen tallafawa mahaddata Alƙur’ani da masu shiga gasar, koda yake ba ita ce ta shirya gasar ba.
Gwamnan ya bayyana fatan cewa a shekarar gaba Jihar Kano za ta mamaye dukkan matakai na irin wannan gasa, yana mai kira ga malamai da su ƙara himma wajen horas da almajirai tare da tabbatar da tarbiyya nagari.
A wani ɓangare na jawabin nasa, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta gano wata baiwar Allah mace da ta shafe kimanin shekaru 40 tana hidimtawa harkar addinin Musulunci, inda ya ce za a duba hanyoyin da suka dace domin tallafa ma ta da ƙarfafa irin wannan hidima mai albarka.
Haka kuma, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiki kafaɗa da kafara da Masarautar Kano domin tabbatar da cigaban jihar.
Dangane da matsalolin rashin tsaro da shaye-shaye, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen kawo sauyi ta hanyar tsare-tsare na musamman domin kare rayuka da tarbiyyar matasa.
Game da batun sauyin sheƙa kuwa, gwamnan ya bayyana cewa Jihar Kano na gab da samun manyan damar cigaba daga gwamnatin tarayya, yana mai cewa duk wanda ya ji irin ayyukan alheri da jihar za ta amfana da su zai yi mamaki.
Daga cikin manyan ayyukan da Kano za ta rabauta da su akwai aikin layin dogo (titin jirgin ƙasa) a cikin birnin Kano, wanda gwamnatin tarayya za ta aiwatar, kuma darajarsa ta kai sama da Naira tiriliyan ɗaya.
