Kano: An bayyana Injiniya Abubakar Kabir a matsayin garkuwar al’ummar Bichi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An bayyana Ɗan Majalisar Wakilai mai Wakiltar mazaɓar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi a matsayin garkuwa ga Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano.

A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata da Ɗan Majalisar Dokoki ta Jiha, Alhaji Lawan Shehu Bichi ne suka bayyana haka a wajen ƙaddamar da sake gina Makarantar Firamaren Hagagawa da dan majalisar ya sake ginawa tare da mayar da filin wasa na Hagagawa zuwa na zamani dukkaninsu a garin Bichi.

Shugaban ƙaramar hukumar da Ɗan Majalisar jiha, sun bayyana cewar irin ayyukan da Ɗan Majalisar Tarayyar ke aiwatarwa a sassan karamar hukumar, musamman ta fuskar ilimi da lafiya da tattalin arzikin bunkasa kasuwanci da tituna da sauran ayyukan raya kasa abin alfahari ne ga al’uma, sun kuma ba da tabbacinsu na cigaba da ba da goyon baya ga dan majalisar domin ci gaba da samun nasarar dukkan al’amuran da ya sa a gaba.

“Yau ga mu Allah ya amsa addu’a za mu hadu a akwati daya kuma in sha Allahu za mu zazzagawa Ɗan Majalisar Tarayya, Abban Bichi kuri’a a shekara mai zuwa ta 2027 fiye da wadda yake samu a da.” Alhaji Hamza Sule Mai Fata

“Injiniya Abubakar Kabir Abubakar! Ba abin da za ka yi sai dai ka kara yi wa Allah godiya. Kuma mu na ba ka tabbacin cewa; muna nan ba gudu ba ja da baya domin duk inda ka je mun san alheri za ka zamar wa wannan karamar hukuma tamu ta Bichi tare da jihar Kani da ma kasar Nijeriya baki daya.”

Da yake jawabi, babban bako mai jawabi a wajen taron kuma tsohon Babban Sakatare a ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Musa Yahya Bichi, ya tabo tarihin kafuwar makarantar ta Hagagawa, inda ya ce, an kafa ta tun alif tari tara da ashirin da tara (1929) wadda ta samar da manyan mutane wadanda suka yi shuhura a matakai daban-daban na gwamnatocin tarayya da jiha da kananan hukumomi.

Daga nan kuma ya lasafta wasu daga cikin manyan mutanen da makarantar ta samar da suka hadar da; tsohon Karamin Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Alhaji Ahmad Garba Bichi da tsohon Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, wato DSS Alhaji Yusuf Magaji Bichi da mahaifin Dan Majalisar Tarayyar ta Bichi, marigayi Alhaji Kabiru Abubakar Bichi, wanda ya taba zama Dan Majalisar Jiha kuma tsohon kwamishina a jihar Kano har sau biyu.

Tun da fari a jawabinsa, Shugaban Kwamitin Ilimi da Dan Majalisar Tarayyar ya kafa a karamar hukumar, Dakta Habibu Usman Abdu, ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da dan majalisar ya samu ta fuskar ilimi, wadanda suka hada da; gina ajujuwa a makarantu daban-daban dake karamar hukumar da ba da tallafin karatu tun daga firamare har zuwa jami’a da daukar malamai a makarantun faramare daban-daban a karamar hukumar da kuma tallafa wa makarantun Allo da na Islamiyya dake sassan yankin.

Da yake bude makarantar ta Hagagawa wadda ya sake gina ta ta koma ta zamani a kan miliyoyin kudi, Dan Majalisar Tarayyar kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi a Zauren Majalisar Tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi, ya bayyana ba shi da wani buri illa ciyar da al’uma gaba.

“Wannan shi ne burina! Wanda ake ganin bai isa ba mu taimake shi da taimakon Allah. Wannan shi ne muhimmu ga kowane shugaba ya tabbatar cewa al’umar da suka zabe shi sun sami cigaba a dukkan yankunansu.”

Sauran wadanda suka yi jawabai a wajen taron, akwai Shugaban Jam’iyyar APC na karamar hukumar da mai kula da Shiyyar Arewacin Kano, Alhaji Sule Ara da Alhaji Sani Mukaddas, inda a karshe kuma aka mika kyaututtuka daga al’umomi daban-daban ga Dan Majalisar Tarayyar, Injiniya Abubakar Kabir Abubakar Bichi, sakamakon jin dadin irin ayyukan da yake aiwatarwa a dukkanin sassan karamar hukumar.

By Babaji