DAGA JOHN WADA a Lafia
Wata ƙungiya da ake kira Renewed Hope Support Group a turance ta naɗa shugaban al’umma a Karu jihar Nasarawa Alhaji Isah Kogi a matsayin Ambasadan zaman lafiya a shiyar Arewa ta tsakiya da birnin tarayya Abuja wato North Central Peace Ambassador a turance.
Ƙungiyar ta Renewed Hope Independent Support Group Committee ta karrama basaraken da muƙamin ne a gidan gwamnatin jihar Nasarawa da ke Lafia babban birnin jihar a makon da ake ciki, inda abokan arziki da iyalai na kusa da basaraken da al’ummar ƙaramar hukumar ta Karu da sauran su suka halarta.
Da yake gabatar wa Alhaji Isah Kogi lambar yabon na musamman, shugaban fannin gudanarwa na gidan gwamnatin jihar, Ishaku Yakubu Kwara ya bayyana cewa karramawar an yi wa basaraken ne bayan an gano shi ya cancanta da muƙamin idan a ka yi la’kari da gagarumin gudumawa da yake bayar wa wajen ɗorewar zaman lafiya da cigaban al’ummar sa da yankin arewacin ƙasar nan baki ɗaya.
Ya buƙaci wanda aka karrama ya tabbatar kwalliya ta biya kuɗin sabulu musamman ta cigaba da aiki tuƙuru wajen cigaban kyawawan tsare-tsare da manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu musamman a yanzu da ake shirye shiryen zaɓukan shekarar 2027 dake tafe.
A nasa ɓangaren wanda aka naɗa wa muƙamin wato Ambasada Alhaji Isah Kogi ya bayyana godiyar sa dangane da karramawar da akayi masa inda ya kuma yi alkawarin cigaba da gudanar da shugabanci nagari wa al’ummar sa musamman mazauna yankin Arewa ta tsakiya da birnin tarayya Abuja, inda ya kuma buƙaci al’ummar nasa baki ɗaya su cigaba da ba shi cikakken goyon baya don samun nasara.
Wakilin mu ya kuma ruwaito cewa wasu daga cikin manyan baƙi da abokan arziki da ‘yan uwan basaraken da suka halarci taron mai tarihi sun haɗa da Kabiru Wakili da Rev. Dr. Emmanuel Akawu Zakwoiyi da Mallam Umar Farouk da Bashir Umar Danmalikin Masaka wanda shima aka naɗa masa muƙamin mai taimaka wa gwamna na musamman a lokacin taron da Babangida Abdullahi da kuma Imran Asifa mataimakin shugaban al’ummar Yarbawa dake garin Masaka a jihar da sauran su inda duk suka taya sabon Ambassadan murnar naɗin nasa tare da bayyana shi a matsayin wanda ya dace da muƙamin kuma zai kawo haɗin kai da cigaban al’ummar Arewacin ƙasar nan baki ɗaya.
A ƙarshe suma Iyalan basaraken da suka halarci taron wato gimbiya Jamila Isah da Yarima Abubakar Sadig da Fatima Isah duk sun godewa kwamitin ɗin dangane da karramawar da suka yi wa mahaifin su.
