Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi kuma shugaban kwamitin shirye-shiryen bikin al’adun da suka shafi tu’ammali da ruwa na RIGATA da a ke yi shekara-shekara a garin Yawuri, Alhaji Yakubu Bala (Tafidan Yawuri, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ranakun 4 zuwa 7 ga watan Fabrairun wannan shekarar a matsayin ranakun gudanar da wannan bikin.
Da yake jawabi, sakataren Gwamnatin ya bayyana cewar bikin al’adun gargajiyar Rigata daɗaɗɗen biki ne mai cike da tarihi a masarautar ta Yawuri dake jihar Kebbi.
Haka kuma ya bayyana cewa bikin wani sashe ne na nuna irin al’adun gargajiyar al’ummar masarautar Yawuri wanda ke ƙunshe da haɗin kai da kuma bunƙasa yawon buɗe ido da bunƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin dama jihar Kebbi da kasa baki ɗaya.
Sakataren Gwamnatin ya kuma gutsuro tarihin bikin na Rigata wanda ya shafi nuna jarunta da kuma sarrafa jiragen ruwa (Kwale-kwale) da tsere da kuma nuna kayan abincin da al’ummar yankin suke nunawa da dai sauransu wanda a ɗauki shekaru da dama ana gudanar da shi wanda yake janyo al’umma da dama daga yankuna masu nisa domin yawon buɗe ido da kuma kasuwanci daga ciki da wajen jihar Kebbi.
Haka kuma ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace tare da ɗaukar dukkanin matakan tsaro na rayuka da dukiyoyin al’umma da suka dace don ganin an kammala bikin lafiya.
Tafida ya yaba wa masarautar Yawuri da gwamnatin jihar Kebbi bisa sake farfaɗo da wannan bikin al’adun gargajiya na Rigata mai daɗaɗɗen tarihi domin bunƙasa tarihi da al’adun al’ummar masarautar Yawuri.
Bikin al’adun gargajiyar Rigata ya kasance ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al’adun gargajiyar al’ummar jihar Kebbi wanda ke nuna irin tarihi, haɗin kai da jarumtar al’ummar jihar masarautar Yawuri.
