
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike, ya yi barazanar cewa nan gaba za su shiga cikin Filin wasa na Yakubu Gowon da ƙarfi sakamakon zargin da ya yi wa gwamnatin jihar Ribas da hana jakadun Sabunta Fata shiga filin.
Wike ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da kodinetocin ƙungiyar na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar.
Ya ce, sun nemi a ba su damar gudanar da taron nasu a filin, amma gwamnatin jihar ta ƙi amince wa buƙatarsu, don haka ya ce nan gaba za su taro filin ko ba da amincewarta ba ta hanyar kutsawa da ƙarfi.
Ya bayyana cewa, a matsayin na ‘yan jihar Ribas babu dacewa a riƙa nuna musu wariya akan ‘yancin da dokar ƙasa ta ba su, saboda muddin aka sake hana su izinin shiga filin, za su ƙwata da ƙarfi.
Tsohon gwamnan na Ribas ya kuma kirayi mambobin ƙungiyar da su kasance masu juriya daga kyarar da suke fuskanta daga gwamnatin.
To saidai duk da wannan ikirari na ɓangaren ministan Abujan, gwamnatin Ribas ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Labaranta, Honour Sirawoo, ta ƙaryata batun wanda da kira da ƙirƙirarren zance da ake nufin ruɗar da jama’a da shi, kamar yadda ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a.
A cewarsa, matakin gyaran da ake yi wa filin a yanzu bai kai yadda za a bada damar gudanar da kowane irin taro a cikinsa ba, saboda babu tsaro acikin hakan.
